Daga lokacin samun yancin kan. Nigeria kawo yanzu an kashe daga da yawa daga cikin shugabannin Nigeria akan karagar mulki. kama daga kan shuwagabannin kasa, ministoci, gwamnoni, komishinoni da dai sauransu.
1- Murtala Muhammad
An kashe Janar Murtala a ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 1976 – Lt. Col. B Dimka shiya jagoranci kisan tsohon shugaban kasar – Ya samu hadin kan wasu manyan Najeriya da kuma kananan hafsoshin sojoji domin tsara juyin mulkin Yadda aka kashe General Murtala Muhammad.
Ranar 13 ga watan Fabrairu na shekarar 1976, na daga cikin ranakun da suka canja tarihin Najeriya saboda a wannan ranar ce aka yi yunkurin kifar da gwamnatin Marigayi Janar Murtala Ramat Mohammed.
A lokacin da aka kama Dimka kuma aka yanke masa hukuncin kisa, ya zayyana yadda suka shirya juyin mulkin da kuma yadda suka samu nasarar kashe Murtala inda ya nuna cewa tun a watan Janairu na shekarar 1976 suka fara shirya makarkashiyar, bayan ya sadu da wasu manyan mutane wanda ya hada har da Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Yakubu Gowon wanda a lokacin yake gudun hijira a London bayan an tunbuke shi daga mulki. Dimka ya ci gaba da cewa, a lokacin ya samu hadin kan kananan hafsoshin soja bisa yadda ya tsara tun farko na kin saka duk wani babban hafsan soja cikin shirin juyin mulkin, inda ya kara da cewa sun tuntubi Janar Bisalla wanda ya ba su karfin guiwar cewa duk abin da zai faru kada su janye batun kifar da mulkin, inda ya nuna masu cewa yana cikin majalisar koli ta mulkin soja amma a duk lokacin da za a yi zama sai a tura shi wani aiki.
Dimka ya kara da cewa sun tsara kashe manyan hafsoshin soja bayan shi kansa Shugaban Kasa, Murtala Mohammed da Mataimakinsa, Cif Olusegun Obasonjo kuma wadannan manyan sojojin sun hada da, Janar T. Y Danjuma, Kanal Ibrahim Badamasi Babangida, Kanal Bajowa, Kanal Mohammed, Kwamandan rundunar Shiyyar Sokoto, Kanal Ibrahim Taiwo sai Kanal Jemibewon da ke rike da rundunar Ibadan sai Kanal Abdullahi da ke jagorantar rundunar shiyyar Jos.
Dimka ya fayyace yadda suka samu nasarar kashe Murtala inda ya ce a Ranar 13 ga watan Fabrairu na shekarar 1976 shi da wasu daga cikin bijirarrun sojojin sun yi kwantan bauna a daidai kan titin George da ke Legas inda Murtala zai bi ya wuce daga barikin ‘Dodon Barracks’, wanda a lokacin nan ne Fadar gwamnatin mulkin soja, inda ya ce a lokacin da motar da ke dauke da Murtala ta doso inda suke labe sai kaftin Maliki ya ba su alamar tasowar tawagar Shugaban kasar wanda a cewar Dimka a lokacin da motar ta wuce inda yake bai ganta ba, saboda a lokacin yana Magana da wasu sai da aka ankarar da shi.
Dimka ya ci gaba da cewa, sun bi motar daga baya inda suka datse ta a daidai wani gidan man fetur da ke titin ‘Bank Road’ wanda daga nan ne, suka fara harbi kuma suka samu nasarar kashe Murtala Mohammed da dogarinsa, Lt. Akintunde Akinsehinwa da kuma direban motarsa. Dimka ya ce bayan sun kashe Murtala, ya tafi gidan rediyo ya bayar da sanarwar juyin mulki. Sai dai kuma an samu nasarar murkushe juyin mulkin inda aka yankewa Dimka shi da wasu mutane bakwai hukuncin kisa kuma aka zartar da hukuncin a ranar 15 ga watan Mayu na shekarar 1976, kuma a lokacin har da Gwamnan jihar Benue Plateau, Joseph Gomwalk.
2. Tafawa balewa
Kamar yadda tarihi ya nuna, mutumin da ya jagoranci bijirarrun sojojin da suka kashe manyan ‘yan siyasar jamhuriya ta farko shi ne, Manjo Emmanuel Ifeajuna wanda dan Kabilar Igbo ne kuma tun yana dalibinsa a jami’ar Ibadan kafin ya shiga soja ya yi fice wajen tsageranci domin shi ne ya jagoranci tarzoman da daliban jami’ar suka yi a 1956 na nuna adawa da ziyarar Sarauniyar Ingila.
A daren da suka shirya makarkashiyar kashe su Marigayi Tafawa Balewa, shi Manjo Emmanuel ya jagoranci bijirarrun sojojin su 22 wadanda kuma dukkanin su, ‘yan Kabilar Igbo ne. Bayan sun isa marabar Onikan, sai ya raba sojojin gida uku. Rukunin sojojin na farko a karkashin jagorancin Lt. G Ezedigo, an ba su umarnin cafko Ministan kudi na wancan lokacin, Cif Festus Okotie-Eboh.
Sai rukuni na biyu a karkashin jagorancin Onyeacham, su kuma ya ba su umarnin kula da motocinsu tare da tabbatar da cewa babu wata mota da za ta wuce ta marabar ba. Yayin da shi Manjo Emmanuel ya jagoranci sojojin da za su kai samame gidan Marigayi Tafawa Balewa kuma a bisa al’adarsa, ba kasafai Marigayi Tafawa Balewa ke amincewa a aje masa jami’an tsaro a gidansa ba ko in zai yi tafiya.
Sojojin da Manjo Emmanuel ya je da su gidan marigayin, ba wadanda aka horas da su ba ne don yaki. A lokacin da suka isa gidan marigayin, Manjo Emmanuel ya sa kafa ya haura kofar shiga gidan bayan da marigayin ya tambayi ko su wane ne a waje. Yana shiga cikin dakinsa, sai Manjo Emmanuel ya nunawa marigayin bindiga kuma ya ce sun zo ne don su cafke shi.
Sai Marigayi Tafawa Balewa ya nemi izininsu kan ya sanya tufafi inda ya saka farar jallabiyarsa ya kuma dauki Casbaha sannan suka tasa keyarsa gaba wanda a tsakanin mintina talatin sun cimma bukatarsu na cafke marigayin ba tare da harba ko da harsashi guda ba. A lokacin da suka iso inda suka aje motocinsu, wancan tawaga da aka ba umarnin cafko Ministan kudin, sun rigaya sun kamo shi a daure.
Sai suka tafi da su kuma bayan sun yi tafiya na wani dan gajeren lokaci sai Manjo Emmanuel ya bayar da umarnin a tsaya inda ya umarci Marigayi kan ya fito daga cikin motar, tamkar ya ba shi damar ya arce wanda kuma bayan marigayin ya fara sassarfa cikin jejin da ke kusa da hanyar sai Manjo Emmanuel ya dauko bindiga ya rika harbinsa har ya samu sa’a ya bindige shi har lahira wannan shi ne karshen rayuwar Marigayi Abubakar Tafawa Balewa a hannun wadannan ‘yan kabilar Igbo. Allah Ya jikansa da RahamarSa.
Daga karshe dai an samu damar kama manjo Emmanuel Ifeajuna sannan aka yanka mishi hukunci kisa daga nan aka zartar da shi.
3. Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto
Direban sardaunan sokoto shi ya bada tarihin yadda aka kashe mai gidansa.
A labarin da ya bada yace Bayan Sallar Asham, sai Firimiya ya sauko daga sama ya shaida mana cewar kowa yana iya tafiya ya kwana cikin iyalansa, sai daya daga cikin hadimansa da ake kira Jarumi, yace shi yana nan ko bukatar gaggawa zata taso. Ni kuma ina tare da a iyalina a gidan Gwamnati a bangare na, da Misalin karfe daya na dare, ina wanke mota a lokacin, sai Firimiya ya sauko yana kwalawa me askinsa kira, yazo da sauri, da yazo sai ya gaya masa yana son yayi masa aski a daren. Sai ya tambayeni da su wa yaga ina magana dazu? Sai nace masa da ‘yan sandan da suke gadin gidan Gwamnati muke magana.
Ashe ban sani ba, nayi kuskure, mutanan da na zata masu gadi ne, ashe sojoji ne, tuni sun shigo gidan a sace, sun rarraba kansu kusfa kusfa. Daga nan Firimiya ya aiki Bakura ya sayo masa kilishi da balangu, daga nan Firimiya yace na zo, na hau sama na daukowa masu gadin Lemo su sha, na shiga na dauko musu ‘Tango’.
A wannan lokacin bamu sani ba ashe, tuni wadannan sojojin sun kashe masu gadin gidan Gwamnati, suna gani na, suka kirani suka ce nai maza maza na bar gidan, kafun na tafi sai daya daga cikinsu yace mun ‘ina Sardauna yake’ Sai na nuna masa ban san wa yake tambaya ba, a lokacin wajen karfe daya da rabi na dare, sai ya sake tambaya ta, ina Sardauna yake, nace musu, tun da yamma da muka dawo daga Hamdala ban mu sake haduwa ba.
Su uku ne, sojojin, sai daya daga cikinsu yace, sun bani dakika biyar na fada musu inda Sardauna yake ko su kashe ni. Sai nayi karfin hali, nace musu, kuna iya kashe ni idan kun so, sai suka kyale ni suka shiga cikin gidan suna neman dakin da yake, a lokacin nan sun duba ko ina basu ganshi ba, daga nan suka shiga sashin da iyalansa suke, suka fito da su waje, suna tambayarsu ina Sardauna yake, ana haka, sai iyalan Firimiya suka garzayo inda nake suka hadu da iyalina. Sai kawai muka fara jin sojojin suna harbi ratata, na kirga harbi yakai sau goma, daga nan suka budewa dakina wuta a zaton su Firimiya yana ciki, suka karya Kofa suka shiga, suka farfasa gilasai, suka birkita dakin amma basu ga Firimiya ba.
Daga nan sojojin suka shiga harbin kan mai uwa da wabi, anan ne fa, iyalin Firimiya suka shiga kururuwa, Inno matarsa, tana ta cewa, Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, daga nan, sai daya matar tasa Hafsatu ta hango Firimiya sanye da doguwar Jallabiya kansa babu hula yana tsaye, sai tayi sauri ta mika masa mayafinta, ta ce ya lulluba yayi basaja ya gudu. Sai Firimiya yace mata, ba zai saka ba, ai shi suke nema kuma gashi. Nima na tashi da sauri na karasa inda Firimiya yake, na kamo hannunsa, amma ina ya dage.
A lokacin nufi na shi ne, na kamo shi, na jashi zuwa dakina na boye shi, tunda sun tabbatar baya ciki, amma ina da wani yayo harbi sai na wuntsula na bar Firimiya a tsaye. A lokacin sojojin suka kashe wutar gidan gaba daya, sai Inno ta taso a guje dan ta zo inda Firimiya yake, ashe wani soja ya hango ta, kawai sai ya biyo ta a baya, yana fadin, Ina Sardauna yake, jin haka sai Firimiya yayi magana yace gani nan, Allahu akbar! Anan wajen Ajalinsa ya sauka, Firimiya yana tsaye kusa da wani makewayi, matarsa Hafsatu ta rukunkumeshi, sojan kuwa, fadi yake ta sake shi ko ya bude musu wuta gaba daya, amma ina Ajali yayi kira, bata ko saurare shi ba. Ta gayawa sojan ka kashe ni tare da shi, daga na kuwa bai yi wata wata ba ya bude musu wuta su biyun, akan idona, Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto aka kashe shi tare da matarsa Hafsatu a lokacin.
Kalli a bidiyo 👇👇👇👇👇