SHARHI

Labarin jaruman kannywood da suka yi soyayya mai zirfi a sakanin su amma basu kai ga aure ba

Jaruman kannywood da suka yi soyayya mai zurfi a sakaninsu har suka rabu basu yi aure ba.

Da yawa daga cikin karuman kannywood maza da mata suna soyayya a sakaninsu amma basu fiye nunawa duniya ba, a yau mun kawo muku jerin jaruman kannywood da suka yi soyayya a sakaninsu amma basu kai ga aure ba.

 

1. ADAM A ZANGO DA NAFISA ABDULLAHI

A shekarar 2015 Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisah Abdullahi, ta yi ta-maza, inda ta ce tana matukar kaunar abokin aikinta, jarumi Adam Zango.

Tauraruwar — wacce ta bayyana matsayinta a shafinta na Instagram — ta kara da cewa tana fatan Allah zai zaba masu mafi alheri tsakanin ta da shi.

Nafisa Abdullahi da adam a zango dai tun kafin jarumar ta bayyanawa duniya tana son Adam a Zango mutane sun san da cewa akwai soyayya mai karfi a sakaninsu.

Bayan nafisa Abdullahi ta bayyana soyayyar ta ga Adam A. Zango, shi ma ya bata amsa ya ce ya yi matukar farin ciki da abokiyar aikinsa, Nafisa Abdullahi ta ce tana matukar kaunarsa. Sannan shi ma yana kaunar Nafisa yana fatan Allah ya zaba musu mafi alheri a tsakanin su. Nan labarin soyayyar su ya karade duniya. Inda ake sa ran watarana zasu yi aure.

Sai a shekarar 2019 da BBC Hausa tayi hira da nafisa Abdullahi ta bayyana cewa basa tare a yanzu tace Kusan shekaru hudu ke nan ko biyar basa tare, kamar yadda Allah ya hada haka kuma yanzu ya raba su. Zama ne kawai ya zo karshe”.

Duk mai ƙallan finafinan kannywood yasan da cewa nafisa da adam a zango sun sha fitowa a finafinai a tare.

 

2. MARYAM JANKUNNE DA SANI DANJA

Maryam jankunne tana daya daga cikin manyan jaruman kannywood kyawawa da aka yi yayinsu a ashekara 2005 zuwa lokacin da tayi a aure a shekarar 2008, jarumar tayi aiki a kamfanin sani danja a wancan lokacin.

A binciken gaskiya 24 Tv tayi ta gano cewa a wancan lokacin da yawa daga cikin mutane basu san da cewa akwai soyayya sakanin Maryam da sani Danja ba sai kwananan da BBC Hausa suka yi hira da Maryam, nan ta bayyana cewa ta taba soyayya da sani danja Allah bai kai su ga yin aure ba, inda ta bayyana hakan da bakinta.

A wancan lokacin Allah bai ƙaddari auren su ba, sai sani Danja ya auri Mansura isa ita kuma Maryam jankunne ta wari wani, a halin da ake ciki yanzu Maryam jankunne bata gidan mijinta shi kuma sani danja ya rabu da matarsa Mansura isa, mudai Muna fatan cewa zasu sake komawa soyayyar su ta baya har suyi aure.

3. SADIYA GYALE DA BABALLE HAYATU

Baballe hayatu da sadiya gyale akwai soyayya a sakaninsu a baya a yadda binciken mu ya gano.

Kishin-kishin din soyayyar ta su dai ya kara karfi ne bayan da wasu hotunan su suka fita a kafafen sadarwar zamani dauke da su cikin irin shiga ta ma’aurata ko kuma ta masu shirin aure.

A shekarar 2016 inda wani dan kannywood ya wallafa cewa baballe da Sadiya gyale sun yi aure inda aka yaɗa labarin a duniya, daga karshe baballe yazo ya karyata batun inda yace raha ce kawai amma basu yi aure.

Yanzu da ake ciki dai baballe hayatu bai taba yin aure ba ita kuma sadiya gyale ta fita daga gidan mijinta da ta aura a baya.

4. BALARABA MUHAMMAD DA SHU’AIBU LAWAN KUMURCI

Su sun kai ga aure amma basu kai ga tarewa ba.

Balaraba Muhammed da shuraibu lawan kumurci a tarihin kannywood ba’a taba samun masoya kamar su ba, suna bayyanawa zunar soyayya a duk inda suka je, hakan yasa a lokacinsu duk duniyar kannywood aka san da soyayyar tasu, an taba yiwa balaraba Muhammad tambaya a wani tattaunawa da aka yi da ita kan cewa ya take soyayya da dan daba nan tayi murmushi cikin fuskar kunya tace a’a wannan halayyar na dabanci a Film kawai yake yinta amma a zahiri ba haka yake ba mutumin kirki ne Abar mata masoyinta.

Sannan gabanin aurenta da shuraibu lawan kumurci yayi, sai da tayi wani waka na ban kwana ga masoyanta da kuma yaɓa shi mijin da zata aura shuraibu lawan kumurci, bayan an daura aurensu ana kan kaina gidan mijinta tayi hatsari a mota Allah ya karbi rayuwar balaraba Muhammad, tabbas a lokacin kumurci ya shiga tashin hankali sosai kan rashin masoyiyarsa da yayi.

Dannan kasan nan domin kallo a bidiyo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button