TAKAITACCEN TARIHIN KI?
Sunana maimuna abubakar wacce aka fi sani da momi gombe actress a matsana’antar kannywood, an haife ni a garin gombe anan nayi primary school dina anan nayi secondary school dina, dukkanin rayuwata a garin gombe nayi, sai yanzu kuma sana’a ta maida ni garin kano.
YA AKA YI KIKA SAMU SUNA MOMI?
Momi suna ne da na gada a wajen kakata maman baba na, ana kiranta maimunatu to su kuma baza su iya kiran sunan ba, shi yasa baba na yake kira na maimunatu.
KI BAMU LABARIN YADDA KIKA SHIGA KANNYWOOD?
Ta hannun mai gida na Usman Mu’azu na shiga Film, usman ya kasance dan garin Gombe ne kuma yana zuwa har cikin gidan mu, kuma yasan yan uwana, iyaye na da kakanne na, kuma ya zama kamar dan gida, a lokacin ni kuma ina sha’awar yin Film, idan suna aikin su na film, a gida ana saka ni na kai musu abinci, idan na kai abincin sai na zauna nayi ta kallon su, sai watarana nace masa ina so nima na shiga masana’antar kannywood, sai yace ai iyaye na baza su barni ba, sai nace idan kayi musu magana ai zasu barni, da ya lura ina so film sosai, sai yayi magana da mama ta kuma sai ta barni na fara film.
A WANNE FILM KIKA FARA FITOWA ?
Na fara fitowa ne a wani film mai suna sunan ka.
ME YASA AKA FI GANIN KI A BIDIYON WAKOKI?
Kasan kowa da yadda yake, aikin ne yazo da haka
AINA KIKA KOYI RAWA?
Ban koyi rawa a ko ina ba, kawai idan aka ce nayi rawa sai naga ina yi.
KE CE JARUMAR MATA DA HAMISU BREAKER YA YI WAKA DA KE?
Mutane da yawa suna kira da hakan, tabbas munyi wakar “Jarumar mata” da Hamisu Breaker abokin aiki na. Ina farin ciki da wakar domin ban yi sammanin zata kai wannan mataki da ta kai ba.
DA GASKE HAMISU BREAKER SAURAYIN KI NE ?
Nima haka nake ji a baki mutane, amma maganar gaskiya ba haka ba ne, Hamisu Breaker abokin business dina ne.
WAYE SAURAYIN KI A KANNYWOOD?
Gaskiya bani da sauri a Kannywood, sai dai wajen Kannywood.
WAYE SAURAYIN KI NA FARKO?
Bazan iya tunawa ba don tun ina makaranta.
WAYE BESTIE DINKI?
Bestie! Bani da Bestie.
WANE DARAKTA KIKA FI JIN DADIN AIKI DA SHI ?
Darakta da na fi jin dadin aiki da shi, shi ne Sunusi Oskar 442.
WACECE BABBAR KAWARKI A KANNYWOOD.
Ina da kawaye da yawa domin duk abokanan aiki na kawaye na ne.
ME YAFI SA KI FARIN CIKI ?
Abinda ya ke sa ni farin ciki shi ne Ibada da nake yi, duk lokacin da nake ibada sai na ringa jin farin ciki.
ME YAFI SA KI BAKIN CIKI?
Abinda yake sa ni bakin ciki shi ne Rasuwar mahaifiya ta, a duk lokacin da na tuno da mutuwar ta sai na ringa jin bakin ciki.
WANE ABIN FARIN CIKI NE BA ZA KI TABA MANTAWA DA SHI BA?
Abin farin ciki da bazan manta shi ba a rayuwa shi ne ranar da mamata ta rasu, shi ne ranar farin ciki na kuma shine ranar bakin ciki na.
ME YASA RASUWAR MAMARKI YA ZAMA FARIN CIKI?
Saboda ni nayi magana da ita na karshe a cikin yan uwa na, kuma ni kadai nasan irin maganganun da kuma yi da ita, da kuna addu’o’in da tamin, bazan taba mantawa da wannan ba.
TUFAFIN TURAWA KIKA FI SAWA KO NA ATAMFA?
Nafi saka kayan Atumfa saboda Atumba kowa cewa yake yafi yi min kyau.
MENENE BURUNKI NA NAN GABA?
Buri na a rayuwa shi ne naga lokacin da Allah zai nuna min ranar aure na.
KIN TABA YIN AURE?
Eh, na taba yin aure ba karya ba ne, amma ban taba haifuwa ba, nan gaba muna sa sammani in Allah ya yarda.
MUN GODE DA TATTAUNAWA DA KIKA YI DA MU.
Ga bidiyon nan 👇👇👇
Nima Nagode.
abubakaryalo99@gmail.com