TATTAUNAWA

Tattaunawa da Musa mai sana’a akan rayuwarsa da baku sani ba, da yadda ya shigo film

Tarihin musa mai sana'a

YA SUNAN KA?

Sunana Musa Abdullahi mai sana’a.

A INA KA SAMO SUNA MAI SANA’A?

Ni mutum ne mai son yin kasuwa, kuma bana raina sana’a, ni dan gwagwarmaya ne akan harkar sana’a da zan yi don na taimaki kaina, in taimaki rayuwa ta, shi yasa ake kira na mai sana’a, sannan nayi sana’o’i da yawa kala-kala.

ZAKA IYA BAMU TAKAITACCEN TARIHIN RAYUWAR KA?

An haife ni a dala local government, nayi makaranta a adaka special primary school, daga nan na tafi secondary school gwammaja bayan nan kuma ina karatu ina sana’a, amma a lokacin nafi bawa harkar kasuwanci karfi sosai.

SHEKARUN KA NAWA ?

Abinda na rike a kaina, shine a ranar da aka kashe mai tatsine aka haife ni a ranar talata.

KANA DA IYALI?

Eh, ina da iyali, ina da mata guda daya da yara Uku.

SHIN KANA DA NIYAR KARA AURE?

Ban sani ba, dama mata ta ta fada min idan kuka zo tattaunawa da ni na fada muku ita kadai ce matata, kuma ga sakon ta na fada muku.

YAUSHE KA FARA FILM?

Nayi shekaru 23 zuwa 24 a industry.

A WANI FILM NE KA FARA FITOWA A KANNYWOOD?

Film din da na fara fitowa shine film din Ibro Horo, mun yi film din ne a garin Wudil.

FINA-FINAI NAWA KAYI A KANNYWOOD?

Nayi finafinai da yawa.

A CIKIN FINA-FINAI DA KAYI WANI FILM NE KAFI SO?

Film din da na fi so shine fim fin Dan Tijara.

ME YASA KAFI SON SA?

Abinda yasa nafi son sa saboda fadakarwa dake cikin film din, mutane sun yi tayi min challenge akan film din, amma daga baya sun fahimci film din da kuma manufar da yake son cimmawa, saboda a cikin film din na kaiwa mamar mu Police.

MENENE KA SAMU NA CI GABA A KANNYWOOD?

Abu na farko shine muna samu yaɓo daga wajen al’umma akan abubuwan da muke yi, sannan su na yi mana addu’a, wanda suka fahimci abubuwan da muke yi kenan a finafinan mu.

Na biyu kuma duk wa’yanda muka hadu da su masu kaunar mu suna jin dadi, mu ma muna jin dadi.

A WANI FILM KAFI SHAN WAHALA?

Film din da na fi shan wahala a cikin sa shine film din makaru, saboda har kuka sai da nayi akan film din.

A FINAFINAN KA KANA FITOWA A MATSAYIN MAI BARKWANCI, SHIN A ZAHIRI HAKA KAKE ?

Ko a zahiri ni mutum ne mai barkwanci, amma ba a ko da yaushe ba, idan kika ga ana hayaniya da ni to jin yunwa nake.

ME YAKE SA KA FARIN CIKI?

Abinda yake sa ni farin ciki shine na ringa sauraron karatun Alkur’ani, bayan shi babu komai.

MENENE AKA TABA YI MAKA DA YASA KA BAKIN CIKI?

Na so wata yarinya yar uwar mu, kuma a gidan mu ta girma kamar kanwa take a wajena, na so ta sosai a lokacin banda kudi shi yasa bata so ni ba, saboda mata sun fi son mai kudi, basa tunanin komai na Allah ne, sun fi son suga kudi yanzu-yanzu, nayi ta mata hidindimu a baya amma wani mai kudi sai yazo ya aure ta, wannan Abin shi ne idan na tuno sai na ringa jin babu dadi, amma yanzu na yafe mata abinda ta min.

KASASHE NAWA KA TABA ZUWA A DUNIYA?

Bazan miki karya ba, kasa daya na taba zuwa a rayuwata shine Saudiyya.

ME YA TABA FARUWA DA KAI A SAUDIYYA IDAN KA TUNO SAI YA BAKA DARIYA.

Abinda ya taba bani dariya shine, watarana ina dawafi a makka ina kuka ina addu’a kawai sai wata ta taho ta fara kiran sunana Mai Sana’a Dan Allah tsaya mu gaisa, abin ya dan ban haushi amma daga baya sai ya ban dariya, kawai sai na daga mata hannu.

A WANE HALI MASANA’ANTAR KANNYWOOD TAKE CIKI?

Masana’antar kannywood tana cikin matsala, matsalar shine rashin tsari da muke da shi, shi ya kawo mana matsaloli daban-daban a masana’antar kuma an rasa yadda za’a yi ayi maganin matsalar.

MUN GODE DA TATTAUNAWA DA KA YI DA MU.

Nima nagode, Allah ya saka muku da lahairi.

Kalli bidiyo 👇👇

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button