LABARAI

Wani yaro dan shekara 16 ya kashe kansa ta hanyar rataya

Wani yaro dan shekara 16 mai suna Ibrahim Lawan ya kashe kansa ta hanyar rataya a kauyen Kuki da ke karamar hukumar Bebeji a jihar Kano.

Hakimin gundumar Bebeji, jami’in hulda da jama’a na masarautar Rano, Nasiru Habu Faragai, ya ce. ya mika rahoton afkuwar lamarin ga Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa, a yayin taron Majalisar Masarautar a ranar Litinin, 15 ga watan Agusta, 2022.

Ya bayyana cewa Sarkin ya bayar da umarnin a kai rahoton ga ‘yan sandan Majalisar Masarautar don bin diddigin musabbabin rasuwar.

PRO ya shaida wa Aminiya( Daily trust) cewa hakimin kauyen ya yi wa mahaifin marigayin tambayoyi kan ko yaron yana da ”maye ne ko tabin hankali”’

“Sarki ya damu da lamarin, sai ya tambayi hakimin gundumar ko yaron yana shaye-shayen miyagun kwayoyi, ya kuma tambayi mahaifin ko yaron yana da tabin hankali ko kuma suna da wani bacin rai, amma mahaifin ya ce ba ko daya. Ya kuma ce ba ya shan kwayoyi,” in ji Faragai.

Ya kara da cewa Sarkin ya umarci hakiman karamar hukumar da su tashi tsaye wajen gudanar da addu’o’i masu yawa domin gujewa faruwar irin wannan lamari.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button