LABARAI

Abin da ya kamata Najeriya ta yi don magance raɗaɗin hauhawar farashin kaya’

Abin da ya kamata Najeriya ta yi don magance raɗaɗin hauhawar farashin kaya’

Masana tattalin arziki a Najeriya na fargabar cewa za a iya samun karuwar wadanda ke fadawa cikin kangin talauci matukar aka ci gaba da samun hauhawar farashin kayan masarufi, kamar yadda yake faruwa a ƙasar.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumar kididdigar kasar ta ce an samu karin hauhawan farashin kayan abinci da fiye da kashi ashirin cikin dari a cikin watan Agustan da ya gabata.

Hukumar ta ce wannan ne hauhawar farashi mafi girma da aka samu a Najeriya a cikin shekaru goma sha bakwai da suka wuce.

Masana irinsu Dakta Shamsuddeen Muhammad na Jami’ar Bayero ta Kano sun shaida wa BBC cewa wasu daga cikin tsare-tsaren da gwamnati ta bijiro da su na taka rawa wajen ƙara hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.

Ya ba da misali da matakin gwamnati na matse bakin aljihu ” a ɓangaren hada-hadar kuɗaɗe, babban bankin ƙasa ya ƙara ƙudin ruwa sau biyu a jere – an ƙara a watan Yuni da Yuli”.

“Wannan ya jawo dole waɗanda suke rantar ku di su yi sana’a zai zama abin da za su ranta za su biya kuɗin ruwa da yawa kuma wannan zai ƙara tsadar abubuwan da za su sana’anta.”

Ya ƙara da cewa wani dalilin da ya janyo halin da ake ciki shi ne ƙara haraji da gwamnati ta yi kan masana’antu da kasuwanni wanda ya janyo hauhawar farashin kayayyaki.

A cewar masanin, yakin Rasha da Ukraine wani babban dalili ne da ya haifar da tashin farashin kayayyaki a duniya gaba ɗaya – “alkama, man fetur da dangoginsa da iskar gas sun yi tsada.”

Dakta Shamsuddeen ya ce matsalar da za a iya fuskanta sakamakon hauhawar farashin kayan shi ne masana’antu za su iya durƙushewa saboda rashin ciniki sannan za su rage ma’aikata – abin da zai shafi tattalin arziki gaba ɗaya, yawan talauci ma zai iya ƙaruwa a cikin ƙasa, kullum rashin aikin yi da talauci sai ƙaruwa suke sakamakon hauhawar farashin kaya”.

Masanin ya ce matuƙar gwamnati na son taimaka wa al’ummarta, toh kamata ya yi ta sake nazari kan tsare-tsarenta musamman kan haraji sannan babban bankin ƙasa shi ma ya ba da tasa gudummawar domin sauƙaƙa al’amura.

“Idan gwamnati ta ƙara haraji a lokaci guda, bai kamata babban banki ya matse bakin aljihu ta hanyar ƙara kuɗin ruwa ba – wannan zai shafi tsadar tafiyar da masana’antu wanda zai kara sa farashin ya daɗa taɓarɓarewa.” in ji Dakta Shamsuddeen.

Bayanan hukumar ƙididdigar ta Najeriya dai na nuna cewa jihar Kwara ce kan gaba da fiye da kashi 30 cikin 100, sai jihar Ebonyi da Rivers da ke bi mata yayin da Jigawa da Zamfara da Oyo suka kasance jihohin da aka samu hauhawar farashi mafi ƙanƙanta.

Duba Nan:Kalli Bidiyo Yanda Camera Tsaro Ta Tonawa Ƴan Bindiga Asiri A Arewacin Najeriya

Amma kafinnan minene ra’ayoyinka dangane da wanna lamarin ?

Dafatar dai kuna gamsuwa da shirye-shiryemu da muke kawomuku acikin wannan shafin namu mai albarka.

Shin kana buƙatar murinƙa kawomuku irin wayannan abubuwa acikin wannan shafin namu mai albarka kuwa?

Kayimuna comment da ra’ayoyinka dangane da wanna lamarin.

Nasan Cewa Zakuji Daɗin Wannan Shirin Namu Mai Albarka.

Shin Kanada Wani Labari Da Kakeso Muyaɗa Acikin Wannan Shafin Namu Mai Albarka.

Zaku Iyya Bayyana Muna Ra’ayoyinku Dangane Da Bukatar KU. Sannan Ku Nememu Ta Waƴannan Hanyoyin Domin Yin Magana Damu Kai Tsaye.

Email Address: Gaskiya24Tv@gmail.com

Phone Number:08162073107

Whatsapp Number: 08162073107

Facebook Page:Gaskiya24Tv

Youtube Channel:Gaskiya24Tv

Idan kana buƙatar arinƙa sanardakai sababin shirye-shiryemu dazara munɗaura batareda kashiga wannan shafin namu ba. Idan yaune farkon zuwanka wannan shafin. to zakaga wani rubutu ya bayyana kawai sai kadanna alamar ‘ALLOW’ domin yin subscription kyauta.

Idan kuma kashigo kuma bakaga anturama wannan rubutun ya bayyana ba, to kaduba gefen hannun damarka zakaga alamar ƙararawar sanarwa kawai sai kataɓata kai tsaye kana taɓawa wani rubutu zashi bayyana sai kadanna ‘OK’ domin sanardakai dazara munɗaura sabon shirimu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button