FATANKI NAN DA SHEKARA 5
Aure, haifuwa da arziki insh’Allah
MINTI NAWA KIKE DAUKA KINA KWALLIYA
Bancika yin kwalliya ba, wannan ma da nayi saboda za’a yi interview da ni ne.
WANENE SAURAYIN KI A KANNYWOOD
Hmm duk yan uwana ne a kannywood
RADE RADIN DA AKE YADAWA GAME DA KE
Ta girma ta tsufa bata yi aure ba, bata son tayi aure wayannan abubuwan su na daya daga cikin abubuwan da aka fi fada.
YA KIKE JI IDAN AN ZAGE KI
Wani lokaci nakan yi dariya wani lokaci nakan yin kuka, sanna wani lokacin nakan ramawa.
KAYAN KI KALA NAWA NE
Ban sani ba
WANI TUFAFI KIKA FI SO KI SAKA
Nafi sa dogayen riguna sannan nafi son atamfa.
WANI FILM DINKI NE SUNANSHU YA BIKII
Wasu tsayin ana cewa yar maye amma hadiza gabaon din ya danne duk wani sunan finafinaina
KI FADA MANA ABUBUWA UKU GAME DA KE
Ni mutumiyar kirki sanna 9 ce bata cika 10 ba dama ance dan adam ajizi ne, ina kuskure ina laifi sannan na uku zan iya maimaita mutuwar kirki.
TAURARUWAR DA KIKA FI SO
Akwai wata a america tana yin programmes tana taimakawa al’umma ta hanyoyi da dama.
WANI WAKA CE KIKA FI IYAWA
Sai dai nace mawaka su yi hakuri babu wata waka da ta tsaya min akai, sai dai wani lokacin idan aka saka waka zan iya binta idan aka katse kuma bazan iya binta ba.
FINAFINAI NAWA KIKA YI
Bazan fada maka iya finafanan da nayi ba.
TALAKA KOMAI KUDI KIKA FI SO
Hhhhhhhh ehh duk wanda Allah ya bani.
WACECE AMINIYAR KI A KANNYWOOD
Duk yan kannywood kawaye nane.
SHIN ZAKI BARI MIJINKI YAYI MIKI KISHIYA
Ko da baka yarda ba Allah ya bashi ikon ya auri mata hudu, to me yasa zaka hana abinda Allah ya halatta sai dai ka yi hakuri
IDAN BAKYA YIN FIM ME ZAKI YI
siyar da kaya Ko mamalkiyar shagon abinci da saura .
A WATA NAWA KIKA KOYI YAREN HAUSA
Baka iya gane iya lokacin da kake koyan yare, wasu kalmomin zuwa maka kawai suke sanna su karu. Daga lokacin da nazo a lokacin na koya kuma har yanzu ina kan koya.
WACCE CE BOYAYYIYAR BAIWARKI
Babu
WANE NE BABBAN JARUMIN KI A KANNYWOOD
Shi ne Rabilu Musa dan Ibro A llah ya gafarta masa.
WANNE FIM DINKI KIKA FI SO
Kamar yadda nasha dukkan finafinai ina son su, shi film wani abu ne da ake kawo maka ka karanta watakila a kalla an kawo maka guda goma ne sai ka zabi guda daya to wannan wanda ka zaba shine kafi so ne, saboda yawancin finafinan da nayi ina son su saboda sai na zabe su nayi su.
DA WAYE KIKA FI A HADA KU A FILM
Ya dangata da producer da yanayin fim din, gaskiya bani da zabi nidai kawai abinda nake gani duk wanda aka hada ka shi kayi kokari kaga ka bada abinda ake so.