TATTAUNAWA

Tattaunawa da Maryam Yahaya, ina jin bakin ciki idan na tuna zan mutu.

Za ki iya bamu takaitaccen tarihinki ?

Suna na Maryam Yahaya, an haifeni ne a garin Kano, a uguwar goron dutse. Nayi primary school dina a yalwa primary school, sannan na secondry school a janguza.

Ya akayi kika fara fim ?

Yadda akayi nafara fim shine gaskiya tun ina yarinya ina sha’awar fim, sai Allah ya cika min burina. Ina farin ciki sosai, gaskiya ina matukar farin ciki. Kuma ina kara godewa Allah.

A wace shekara kika fara fim ?

Eeh to, nashiga harkar kannywood a shekarar 2016, kuma na fara da fim mai suna “Mansoor” .

Kin yi fina-finai sun kai nawa yanzu ?

Gaskiya bazan iya tuna adadin fina-finan da nayi ba.

A fina-finanki wanne kikafi so ?

Duka fina-finai na ina son su. In kaga nayi fim, to ina son shi.

A wane fim ne kika fi shan wahala ?

Gaskiya fim din da nafi shan wahala shine “Mariya”. Domin a kwai wata faduwa da nayi ma, a gaske nayi faduwar. Na ji ciwo sosai.

Me yake sa ki farin ciki ?

Gaskiya abin da yake sa ni farin ciki, abu ne guda daya. Abun da yake saka ni farin ciki shine naga ‘yan uwa na suna cikin farin ciki.

Me yake sa ki bakin ciki ?

Abin da yake saka ni bakin cikin irin in ta tuna watarana zan mutu in koma ga ubangiji na

Wane irin abinci kika fi so ?

Abinci ? Gaskiya, ina son tuwo da miyar kubewa danya.

Wace ce babbar kawarki ?

Ai ni ba ni da babbar kawa a kannywood. Babbar kawata ita ce mahaifiyata. To kaga dai ina da yayye mata a kannywood kuma ina da iyaye mata. To kaga dai dukkan su yayye na ne , iyayena kuma kawayena ne sannan abokan shawarana ne.

Wace tambaya aka fi yi miki ?

Eh to gaskiya in an hadu da ni, an fi tambayata kan fina-finan da nayi.

Wace amsa kike ba su ?

Daidai da tambayar da suka yi min.

Turare da sarka da takalmi, wanne kika fi so ?

Turare

Wadanne kasashe kika taba zuwa ?

Na je Saudiya, na je Dubaï, Gambiya, Nijer da dai sauransu…

Wace kasa kike fatan zuwa ?

Amerika

Wace kasa kika fi jin dadin zuwa ?

Gaskiya babu kasar da nake jin dadin zuwa irin Saudiya. Ko yanzu ina son inje ta.

Mene ne babban fatan ki a Kannywood ?

Mu rabu lafiya da kowa. Nima naje nayi aurena.

Abya kin dauke kafa daga Kannywood saboda rashin lafiya, ya ake ciki yanzu ?

Ni ban dauke kafa daga kannywood ba. Rashin lafiya kuma ai tana kan kowa. Ko kai yau zaka iya tashi lafiya gobe kuma katashi ba lafiya. Amma dai ni yanzu alhamdulillah, l’m Ok

Ko Kina siyasa ?

Yanzu ai duniyar ta koma siyasa. Kuma yanzu kaga an bawa matasa da ma suma du fito suyi siyasa. Dan haka nima a matsayina na matashiya nake yin siyasa.

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button