CIN AMANAR TSARON KASA……
‘Yan sanda a garin Benishek na jihar Borno sun kama wani gurbataccen sojan Nigeria mai suna Sergeant Undei Joseph yana da lambar aikin da rundinar sojin Nigeria kamar haka: 02NA/52/3510.
Sojan Yayi dakon tabar wiwi daga garinsu bayan hutun aikinsa ya kare cikin motarsa kirar Acura Jeep dauke da namba kamar haka: Lagos FKJ76, Sojan ya iso har Benishek zai wuce ta inda ‘yan sanda suke duba ababen hawa sai yaki ya tsaya, shine ‘yan sanda suka fasa tayar motarsa da bullet.
Bayan sun kamashi sai wani dan sanda ya shiga motar zai karasa da ita Police station na Benisheik, shine sai wani soja da yake da hannu a dakon tabar wiwin ya bude wa ‘dan sandan wuta ya kashe shi.
Yanzu haka dai rundinar sojin Nigeria ta kama jami’inta da yayi dakon tabar wiwin da wanda yayi harbin, amma a rahoton da ta fitar tace wai harbin bisa kuskure ne.
Dan sandan Musulmi ne, sunansa Sergeant Ahmad Ali, maciya amanar sojoji sun kashe shi a banza da Azumi a bakinsa, na san ba abinda zai faru, already rundinar soji tace harbin wai bisa kuskure ne.
Su kuma shugabanni da ya kamata suyi magana akan wannan cin amanar tsaron Kasa da sojoji sukayi ba zasuce uffan ba don a hukunta sojojin, saboda matsalar bata shafesu ba
Allah Ka isar wa Ahmad Ali, Ka sa ya dace da mutuwar shahada.