Yammata kannywood 5 da suka fi kowace jaruma kudi da more rayuwa da kuma bayanai a kansu.

 

Kannywood tana daga cikin manyan masana’antun finafinai a africa, miliyoyin kudade suna shigarta tun daga lokacin da aka kafata a shekarar 1990, da yawa daga cikin wa’yanda suke ta’ammali da matsana’antar kama daga kam jaruma furodusoshi masu bada umarni da marubuta da dai sauran sun samu alhairai sosai a matsana’antar, musamman mata shi yasa a yau muka kawo muku jarumai mata da suka fi a kannywood.

 

Rahama Sadau

Idan ana maganar masana’antar kannywood to babu kawa dole ne a zayyana sunan wannan jarumar duba da irin ci gaba da kuma nasarori da samu a sanadiyar wannan matsana’antar.

Idan ana maganar Mata 10 da Suka fi Kowa Kudi a masana’antar al-kalumma sun nuna cewa Jaruma Rahama Sadau sune a sahun gaba, domin jaruman ba a matsana’antar kannywood kadai ta tsaya ba tana fitowa a finafinan kudancin Nigeria wato nollywood sannan har ta sallake kasar Nigeriya zuwa kasar indiya domin yin finafinai.

An haifi jarumar a ranar 7 ga watan 7 December 1993 a unguwar Sarki dake cikin garin Kaduna a Najeriya. Rahama Sadau ta shiga a masana’antar Kannywood a shekarar 2013, Jaruma Sadau ta samu fice bayan fitowar ta a wani shiri mai suna “Gani Ga Wane” tare da Jarumi Ali Nuhu.

 

Hadiza Gabon

Hadiza Aliyu wadda aka fi sani da Hadiza Gabon An haife ta daya 1 ga watan Yunin shekara ta 1989 a Libreville dake kasar Gabon. Jaruma Gabon ta samu shiga masana’antar kannywood ne bayan ta bar kasarsu Gabon zuwa jihar Adamawa, daga baya kuma ta tashi daga Adamawa ta koma Kaduna domin shiga a cikin masana’antar kannywood.

Hadiza ta fara fitowa ne a shekarar 2009, cikin wani shiri mai suna “Artabu”. Ayau jarumar na daya daga cikin mata goma 10 dakeda arziki a masana’antar.

Tabbas jarumar tana kan gaba cikin jarumai mata da suka fi kudi a kannywood ko irin rayuwar da take ba irin ta wasu jaruman bane, ta mallaki manyan shaguna da suke shigo mata da manyan kudade sannan bata karbar kasa da miliyan daya idan za’a sanya ta a film kamar yadda ta bayyana

 

Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi Jaruma ce mai dunbin masoya duba da irin kwarewa da takeda ita dakuma nagarta acikin masana’antar jarumar ta kara farin jini a shekarar 2020 da ta fito a shirin labarina kamin a maye gurbin ta da fati washa.

Tabbas jarumar tana da kudi sosai sannan yanzu bata fito zama a kasa Nigeria ba sai kasashen turai, saboda tsada da take da shi idan za’a saka ta finafinai shi yasa ba’a fiye kallonta a finafinai a yanzu ba, sannan kowa ya santa a harkokin business da kuma zamantowa ambassador a kamfanonin daban-daban.

An haifi Nafisa a ranar 23 January 1992. Nafisa ta fara harkar fim tana da shekaru goma sha takwas 18, fim din da ya fito da ita shine “SAI WATA RANA” a 2010.

 

Hafsat Idris

Jaruma Hafsat Ahmad Idiris amma anfi saninta da Hafsat Idris na da kekkyawar siga da kuma kula da jiki duba da irin ‘yayanda jarumar keda.

An haifi jarumar ranar 14 ga watan Julin shakarar alib 1987 a garin Shagamu dake jihar Ogun a Najeriaya. Iyayen jarumar “yan asalin Jihar Kano ne dake Najeriya. Tun kafin shigar jarumar a masana’antar kannywood Hafsat Idris yar kasuwa ce wacce ta kware sosai a kasuwanci na zamani inda take tallata hajarta a shafukan sada zumunta.

Hafsat Ahmad Idris ta fara fim ne a shekarar 2016 inda ta fito a cikin shiri mai suna Barauniya. Hafsat Idris ta mallaki kamfanin samar da finafinan Hausa mai suna Ramlat Investment, sannan tana manyan shaguna a kasuwanni. Tabbas tana daga cikin jaruman kannywood mata da suka fi kudi da yake ita kudin nata ba a film kadai ta samo shi ba domin tun kafin ta shigo film tana da kudaden ta a aljuhu.

 

Amma jarumar tayi aure a shekarar baya.

 

Fati Washa

Jaruma Fatima Abdullahi wadda a kafi sani da Faty Washa na daya daga cikin kyawawan mata a masana’antar kannywood, jarumar tayi fice sosai da kuma nuna kwarewa a duk shirin fim da ta fito, sannan jarumar bata taba yin aure ba wato allurace cikin ruwa. Tabbas tana daga cikin matan kannywood 10 da Suka fi Kowa Kudi a masana’antar ko a film din labarina da take fitowa miliyoyin kudade ake bata ga wasu business da take tare da shagunanta na saida kayayyaki.

An haifi jaruma Faty Washa a ranar 21 ga watan Fabrairu, 1993, a jihar Bauchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *