KANNYWOOD

Tattaunawa Da Umar M Shareef Ya Bayyana Budurwada Yakeso Ya Aura A Kannywood

Tattaunawa Da Umar M Shareef Ya Bayyana Budurwada Yakeso Ya Aura A Kannywood

Tattaunawa Da Umar M Shareef Ya Bayyana Budurwada Yakeso Ya Aura A Kannywood

Acikin Shirinmu na yau munkawomuku takaitacciyar hira tsakanin mawaki kuma jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood waton Umar M Shareef da jaruma Hadiza Aliyu Gabon inda yake amsa wasu muhimman tambayoyi kamar haka:

Hadi.za Aliyu Gabon: umar m sharreef Ada nasan babu ruwanka da siyasa, sai gashi kwatsam naganka da rarara, ko miyasa ?

Umar M Shareef: Ganina tare da rarara ai ba siyasa ɓace tahaɗamu. Minhaɗune a wata haɗuwa da munkayi domin gina wata ƙungiya da zata taimakon kammu dakuma masana’antarmu.

Hadiza Aliyu Gabon: Amma kuma ai gashi naganka kana talata wani ɗan takara gwamnnan kano a ɓangaren Abdul Amart ya akayi haka ?.

Umar M Shareef:Hakan zai iya faruwa saboda Ni ɗan ƙasane waton ɗan Najeriya ne. kuma kano da kaduna da mai duguri da legas duka inada dama nayi abinda nikeso nayi cikinta, saboda haka nazaɓi wannan ɗan takara na jahar kano saboda ina tare dashi, kamar yanda shima yanuna yana tare dani nima, Yakamata inbashi gudunmuwa da zani iya nima.

Hadiza Aliyu Gabon: Aganinka yakamata ace mawaƙi angansa awajen siyasa ?

Umar M Shareef: So ina ganin idan takama infito takara dakaina bama inwaƙe waniba, zan iya.

Hadiza Aliyu Gabon: zakayi siyasa Amatsayinka na mawaki, zai iya baka dama idan kaga anyi ba dai-dai ba kafito kayi magana, kokuma idan anyi dai-dai kafito kayi magana?

Umar M Shareef:Kwarai da gaske kuwa, idan anyi ba dai-dai ba, koda wanda na talatane idan takama zan iya fitowa nace anyi ba dai-dai ba, musamman kujeranan da akeyi shekara hurhuɗu. Idan Munkayika daga baya mukaga bakayi abinda muke tunanin kayiwa jama’a ba sai mufito mufaɗa.

Hadiza Aliyu Gabon: Baka tunanin yin magana zai iyasawa karasa abincinka saboda kowane kayiwa waƙa akwai ƴan kuɗaɗen da kake samu ?

Umar M Shareef:kwarai da gaske mana, saboda kafin muhaɗu da kowane ɗan siyasa inacin abinci dan haka rabuwa dashi bazai hanamin cin abincinaba.

Hadiza Aliyu Gabon: Wanene Aminu Ala ?

Umar M Shareef:Aminu Ala wani mawaƙine da duniya tasan dashi.

Hadiza Aliyu Gabon: yakake kallon Aminu Ala ?

Umar M Shareef:Ina kallonshi Amatsayin baban mawaki mai daraja wanda nike girmamashi.

Hadiza Aliyu Gabon: Ana ganinku kamar ba kanku a haɗe yakeba tsakaninku da Abdul M Shareef,Mustapha M Shareef, Minene Gaskiya Lamarin ?

Umar M Shareef:Idan har kammu baya haɗe to baza’arinƙa ganin muna ayuka atareba. nayi album nasake waƙoƙin wanda mafi yawan waƙoƙin Mustapha M Shareef ne Yabada umurni. Asalima nayi sabon Series nawa wanda nake saki a YouTube channel nawa wanda banma fitoba acikiba. abdul M Shareef ne da sauran mutane. Saboda haka idan munada wata matsala bashi yiyuwa yazamana al’amuramu mukeyi atareba.

Hadiza Aliyu Gabon: Har acikin masana’antar anafaɗa cewa kanku ba ahaɗe yakeba.

Umar M Shareef: Gaskiya nidai wannan Magana bantaɓa riskantaba. dama hakan tana iya faruwa ayita maganganu gefe batareda kasaniba. amma ni ba taɓa cin karo da wannan maganar ba.

Hadiza Aliyu Gabon:Actin Da waƙa, wanene kake tunanin kafi iyawa ?

Umar M Shareef:Waƙa

Hadiza Aliyu Gabon:miyasa bakabari Abdul M Shareef yayi Actin kaikuma kacigaba da waƙa?

Umar M Shareef; Ina cikin masana’antar film kusa da shekara goma, nayi producing nayi Actin duk dacewa a mawaƙi anka fara sanina. Acikin finafinai da niyi producing akwai wanda kika fito aciki. actin kuma da nikeyi ban ɗaukeshi kamar ƴanda nikeyin waƙoƙiba.

Hadiza Aliyu Gabon:miyasa ake tunanin kai yaron Abubakar Bashir mai sadda ne?

Umar M Shareef:wayake tunanin haka?

Hadiza Aliyu Gabon:mutane da dama.

Umar M Shareef: Gaskiya Ni ba yaron Abubakar Bashir mai shadda bane, hasalima abokin aiki nane.

Hadiza Aliyu Gabon;kabamu labari yanda rayuwarka take tsakanin aikinka da iyalenka.

Umar M Shareef: inayinta yanda yakamata kasancewa inasamun hutu da nike basu bakin gwargwadon hali.

Umar M Shareef: Ke yakikeyi da naki samarin ?

Hadiza Aliyu Gabon:Ƴanda akeyi haka nikeyi dasu.

Umar M Shareef:To ni yazakiyi Dani ? kuma kinani labarin yanda kikeyi da samarinki.

Hadiza Aliyu Gabon:Samari guda ɗaya nikedashi.

Umar M Shareef:Minene sunanshi? kuma zaki iya auren ɗanfim

Hadiza Aliyu Gabon: Eh mana

Umar M Shareef: wazaki iya aura?

Hadiza Aliyu Gabon:Falalu A Ɗorayi

Umar M Shareef: Miyasa ?

Hadiza Aliyu Gabon: Saboda Falalu A Ɗorayi mutune misali ansanshi da hakuri. Zan iya zama dashi kuma zai iya zama dani.

Hadiza Aliyu Gabon: Misali ace bakayi aureba, wace jaruma kake tunanin zaka iya aura acikin masana’antar Kannywood?

Umar M Shareef: babu amsa.

Hadiza Aliyu Gabon: Wacece Budirwaka a Kannywood ?

Umar M Shareef:babu amsa

Hadiza Aliyu Gabon: Ina maganar aurenka da jaruma Amal Umar yakwana?

Umar M Shareef:lokaci ake jira idan lokacin yayi za’ayi.

Hadiza Aliyu Gabon: kazaɓi daya daga cikin wa’yannan mutane biyu
(1)Ali Nuhu
ko
(2) Bashir mai shadda

Umar M Shareef:Ali Nuhu

Hadiza Aliyu Gabon:Faɗamin abu ukku da kasani game da Ali Nuhu

Umar M Shareef(1):Yafiya
(2)Taimako
(3)Hakuri.

kuma nazaɓi Ali Nuhu ne badun komai ba saidun cewa Ali Nuhu ne nifara sani saboda shine yajamyoni ajikinsa har nasamu wannan ɗaukaka. amma Abubakar Bashir maishadda abokinaneshi kuma abokin aikina.

wannan itace tautaunawa da aka gudanar a atsakaninsu
zamucigaba da kawomuku wata tattaunawa da sauran jarumai acikin wannan shafin namu mai albarka. dafatar dai kunji daɗin wannan shirin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button