KANNYWOOD

Ali Nuhu Kaji Tsoron Allah Ka Tubu Da Jahilci Dakayi~Cewar Malam Abu Jafar

Ali Nuhu Kaji Tsoron Allah Ka Tubu Da Jahilci Dakayi~Cewar Malam Abu Jafar

Shahararren Malamin Addinin Musulunci Malam Abu Ja’afar Yayi kira zuwa ga Fitaccen tauraron Kannywood Ali Nuhu da yayi gaggawa tuba zuwa ga Allah akan abinda ya aikata kafin lokaci yakuremasa acikin wani faifain bidiyo da yafitar jiya Lahadi.

Idan bamu mantaba kwanakin baya da suka gabata anyi hira da Fitaccen tauraron Kannywood Ali Nuhu abisa waƙarsa da yayi inda yake cewa wazaibashi bayan annabi.

Malamin yayi dogon bayani tareda bada manyan hujjoji da suka dace dangane da abinda jarumin ya aikata.

Malamin ya bayyana cewa Kamata yayi Ali Nuhu yayi lidamar abinda ya aikata, amma har kara kafewa yakeyi akan cewa abin da yafaɗi shine dai-dai.

Saboda Babu wanda ake neman taimakonsa bayan Allah Sallallahu wata’ala idan aka shiga wani hali.

Bayan wannan malamin, malamai da dama sunyi masa gyara akan abinda yafaɗi, daga cikinsu sunhaɗa, Malam Tijjani Ahamad Guruntum, Malam Kabiru Haruna Gombe da sauransu.

Yayinda wasu malamai sukaga cewa abinda yafaɗi dai-dai ne, musamman malaman ɗarika.

Wannan lamarin ya janyo cecekuce a faɗin duniya baki ɗaya, wanda hakan yajanyo yin muƙabila atsakanin malaman ƙungiyar izalatul bidi’a Wa’iƙamatu Sunna akan wannan lamarin.

Mai karatu mizakace dangane da wannan lamarin ?

Munajiran amsoshinku awajen comments da munka tanadanmuku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button