Daya daga cikin tsoffin hadiman tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya caccaki mawakin nan Davido tare da zarginsa da yada bidiyon batanci ga Muslunci.
Bashir Ahmad, ya bayyana cewa, Musulmai wasu irin mutane ne da ke mutunta addininsu da ma na wasu, don haka ba sa wasa da addininsu.
Ya bayyana hakan ne bayan da Davido ya yada wani gajeren bidiyon wata wakar da @logosolori ya rera, kamar yadda Legit.ng Hausa ta gani a shafin