KANNYWOOD

Martanin Ameenu saira akan suka da yake samu kan Raba Gardama na shirin labarina

Jagoran shirin fim din labarina mai dogon zango kuma mai bada umarnin shirin Malam Aminu Saira, ya koka akan yadda wasu daga cikin masu kallon fim din suke basu da hakuri sai dai yawan korafe korafe akan wani abu da suka gani wanda baizo dai-dai da ra’ayinsu ba.

Aminu Saira ya Kara da cewa yana jin takaici da bacin rai idan yaga karamin yaro yayi masa rubutu mara dadi dake nuna rashin da’a akan fim din labarina, wanda yace shi yaga dama yake yin fim din idan yaga dama yana iya dainawa baki daya.

Saira ya bayyana hakan ne yayin hirar da akayi da shi ranar Asabar ta cikin shirin Nishadi@360 na Kanawa Radio.

Acewarsa chan chanta ce tasa suka saka jarumin da suka sanya a matsayin Raba-Gardama.

” Naso in danyi tsokana akan Raba Gardama wanda naga yana da “treading” bazan iya zama sama da dubunai sunyi martani wata Allah Wannan tattaunawar tayi yawa a soshiyal midiya a kullum abinda ake so dan kallo ya kama kallon halaye “character” wane mutane da yawa mun zauna “debate” muhawara kenan sosai akan wannan halaye na raba-gardama.

Kuma wasu mutane nayi ta ganin ra’ayoyinsu wanda suna tsammanin za’a dauko wani jarumi sananne a sa a wannn role din bashi bane.

” Aminu saira ya cigaba da cewa abinda munka sani ko abinda muke dubawa shine zatin mutum da yadda munyi “interview” da zai iya sanar da sakon “delivery” yadda muke sonsa sosai “perfectly” ya iya sosai.

Yana iya yi eh to wannan shine daukake ne ko ba daukake bane wannan ba damuwar mu bane kawai waye zai iya tawa rawar “role” din kafin mutane su saba na samu tsauri da shiga wani yanayi kafin yaje wannan role din wallahi nayi istikhara bansan adadi ba.

Allah zaba mana wanda wanda zaiyi fiye da abinda muke tsammani wallahi ina zaune aka kawo na duba clip clip dinsa irin rawar da ya taka “role” mukayi interview dinsa mukaga yayi.- inji shi aminu saira.

Hirar akwai maganganu da yawa amma ga hirar nan ku saurara kuji.

Kalli bidiyon a kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button