Yan kannywood da aka kaisu gidan yari (prison) saboda film da kuma abinda yasa aka kai su

1- NAZIRU SARKIN WAKA

 

Naziru M. Ahmed shi ne sarkin waƙar tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II wanda ya daɗe yana kai ruwa rana da Gwamna Ganduje har sai da aka cire shi daga kan mulki a watan Maris da ya gabata.

An kama naziru sarkin waka ne a watan satumba a shekarar 2019 a bisa laifin fitar da wata waƙa kafin hukumar tace fina-finai ta Kano ta tantance ta, da kuma hadin gwiwan hukumar yan sanda da suke wakiltar gwamnan kano wato ganduje.

Sai dai a farkon abin bayan an bada belin naziru sarkin waka daga baya kotun ta soke belin da aka ba shi inda ta gindaya masa wasu sababbin sharuɗan belin.

Daga nan ne ta aike da shi gidan yari saboda rashin cika sharuɗan a kan lokaci.

A wannan lokacin da aka kara zama sai lauyan gwamnatin jihar Kano, Barrister Wada Ahmad Wada, ya gabatar da wata takardar bayar da haƙuri ga gwamnatin Kano wadda ya ce daga hannun Naziru M. Ahmed ta fito.

A cikin takardar, wadda Sarkin Waƙa ya rubuta ta zuwa ga Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, ya ce “ni Naziru M. Ahmed ina bayar da haƙuri matuka bisa zargin da aka yi mini kuma ina da-na-sanin abin da hakan ya haifar.”

Mawaƙin ya ƙara da cewa ya bayar da haƙurin ne bayan masu ruwa da tsaki sun tsoma baki a cikin lamarin.

An sha zargin gwamnatin jihar Kano da yin amfani da hukumar tace fina-finai ta jihar wajen gallaza wa ‘yan fim da kuma mawaƙan Kannywood da suke goyon bayan masu adawa da ita.

A wannan al’amarin da yawa daga cikin manyan jaruman kannywood irinsu Nuhu Abdullahi, hadiza gabon, nazifi asnanic, ali nuhu, dadai sauransu sun nuna bacin ran sun kan kama mawakin .

 

2- ADAM A ZANGO.

 

Adam a zango ya kasance mawaki ne kuma jarumi ne a matsanatar finafinai na kannywood.

A shekarun baya a lokacin da Ibrahim shekarau yake a matsayin Gwamna a jihar kano, An kama jarumi Adam a zango a sakamakon wani album dinsa da ya fitar mai suna bahaushiya, a cikin wannan album din nasa an zargin Adam a zango da fidda tsiraici a bidiyoyin wakokin nasa musamman a wakarsa na Lelewa wanda a cikin ana iya ganin ga wasu yan mata suna rawa cibiyoyin su a waje, wanda hakan ya tsabawa dabi’ar malam bahaushe da kuma kuma karya dokokin hukumar tace finafinai na kannywood,, gashi kuma ya sakawa wakar tasa suna Bahaushiya. Bisa wannan dalilin yasa gwanmatin kano ta wancan lokacin tasa aka kama adam a zango aka jefa shi gidan yari.

Bayan fitowarsa daga gidan yari adam a zango ya koma garin kaduna da zama inda yayi wani waka mai suna Ayoyo a wakar yayiwa gwamnatin kano na lokacin raddi akan kama shi da aka yi.

Har wa yau adam a zango yana jin zafin wannan daurin da aka masa a gidan yari inda ya tabbatar da hakan a wani hira da bbc hausa suka yi da shi a shirin su na daga bakin mai ita.

 

3- SUNUSI OSCAR

Sunusi oscar 442 ya kasance mai bada umarni ne a matsanatar finafinai na kannywood. Shima dai an kama shi a watan agusta a shekarar 2019 akan sana’arsa na bada umarni a finafinai.

Shugaban hukumar tace finafinai a kano wato Afakallahu yace an kama Oscar ne, wanda yana cikin ‘yan fim din da ke goyon bayan Kwankwasiyya, saboda ya “saba ka’idojin gudanar da sana’arsa a Kano, inda ya saki wata waka wadda akwai badala a ciki” wanda garzali miko yayi mai suna SO NA AMANA.

Ya kara da cewa sun jima suna bibiyar Oscar domin su kama shi, amma sai a ‘yan kwanakin nan ne suka samu damar yin hakan.

Amma a lokacin shi oscar ya musanta zargin da ake masa, yace ba shi ne yayi wakar ba kawai shi umarnin bidiyon ya bada.

amma daga karshe wata kotun kotun majistire a jihar Kano ta bayar da belin darakta Sanusi Oscar a masana’antar Kannywood bayan hukumar tace fina-finai ta gurfanar da shi a gabanta bisa zargin saba kai’dar aiki.

Kama sunusi oscar ya tada jijiyoyin wuya sosai a sakanin yan inda wasu suke giyon bayan sa wasu kuma tsabanin hakan.

 

4- RABILU MUSA IBRO

Marigayi rabilu musa dan ibro ya kasance jarumi ne barkwanci wanda zamu iya cewa babu wanda ya taba irin farin jininsa a jaruman barkwanci na kannywood.

Shima dai an taba kama shi sannan aka kai shi gidan yari kan zargin sa da aka yi na sakin wani bidiyo da ya tsabawa hukumar tace finafinai na kano wanda Rabo yake jagoranta a lokacin da ibrahim shekarau yake gomna a jihar kano.

Shima daga karshe an kyale shi sannan ya dan dau wasu lokuta bai fito a finafinai daga baya ya fara fitowa.

Duk mai kallon finafinan ibro na bayan an sake shi, zai ringa jin lokaci zuwa lokaci yana habaici ga gwamnatin da ta kama shi, Allah yaki kanshi da rahama yasa Aljanna ce makomarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *