Abun da yasa n’a dade a rayé cikin koshin lafiya: hira da dan shekaru 86 .

Abraham Gbodzi dan shekara 86 da haihuwa yana aikin gyaran injin dinki na tsawon shekaru 63, kuma ya bayyana wasu sirrikan abin da ya kara masa karfin gwiwa a tsawon wadannan shekaru.

A wata hira da akayi a SVTV Afirka, Mista Gbodzi ya bayyana cewa kasala rashin lafiya ne, kuma yana haifar da rauni a cikin jiki. Ya kuma shawarci matasa da su rage kayan abinci masu tada hankali.

“Kuna bukatar tafiya kullum; Babban motsa jiki ne. Har ila yau, a rage kayan yaji saboda rashin lafiya. Ya kamata ku girmama wasu kamar yadda kuke girmama kanku.

Yaro  zai girmama ku ne kawai idan kun girmama shi. Kar ku zama masu kwadayin kudi. Yi aiki tuƙuru da samun kuɗi ta hanyar da ta dace.

” Bugu da ƙari, Mista Gbodzi ya ambata cewa matasa ba sa rayuwa mai tsawo saboda kwadayin kuɗi. A cewarsa, da yawa suna son samun arziki cikin sauri ba tare da aiki tuƙuru ba.

“Ku yi hankali da hakan, kuma za ku daɗe. Hakanan, duba yadda kuke sarrafa kuɗin ku kuma ku guje wa masu haƙa gwal. Za su yi kamar suna son ku, amma kuɗin ku ne suke so.

“Mun canza duniya. Abin da Allah ya halitta har yanzu haka yake, amma mutanen da ke cikinta(duniya) ne suka canza yadda al’amura suke.”

”Da yake magana game da aikinsa, Mista Gbodzi ya ambata cewa ’ya’yansa sun ƙarfafa shi ya daina aiki, sai dai hakan ya sa ya n’a jin gajiya da kadaici a gida.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *