Bauchi | Yadda ya kashe budurwarsa mai dauke da cikinsa na wata 4 da aka kasa zubarwa.

An kama wani matashi dan shekara 27 mai suna Munkaila Ado bisa zargin kashe wata yarinya mai suna Safiya Danladi mai shekaru 13 a unguwar Pali da ke karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.

Safiya tana dauke da ciki na wata hudu wanda shi wanda ya kashe ta yayi mata wato mukaila, wanda shi ne saurayinta.

Munkaila ya so a zubar da cikin an kai Safiya a asirce zuwa jihar Gombe domin zubar da cikin.

Daga baya Munkaila ya zabi kashe masoyiyarsa ne bayan yunkurin su ma zubar cikin bai yi ba, domin abu ne mai wuya aci nasarar zubar da cikin da ya kai watanni hudu.

Sai dai wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi (PPRO), SP Ahmed Mohammed Wakil ya saida cewa: “Wanda ake zargin (Munkaila) ya amsa cewa wacce ta mutu budurwarsa ce mai ciki watanni hudu mahaifiyar yarinyar tasan da cikin amma mahaifinta bai sani ba wato Baba Alhaji Danladi Mohammed.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa Munkaila ya hada baki da mahaifiyar yarinyar ‘yar shekara 13 da kuma wani mai suna Mu’azu, inda suka tafi da wanda aka kashe zuwa Gombe domin a zubar da cikin, daga nan suka isa Gombe aka kai ga wata Hajiya. Amina Abubakar ‘f’ yar shekara 50 a Jekada Fari a bayan Asibitin Specialist Gombe inda aka yi wa wacce abin ya faru da wasu abubuwan da zasu haddasa zubar da cikin amma hakan bai yu ba.”

Ya ce yayin da yake komawa gida a jihar Bauchi Munkaila da Muazu sun shake Safiya har lahira inda suka kashe ta a wajen. Daga nan ne suka kona gawar tare da binne ta a wani kabari mara zurfi.

SP Wakil ya bayyana cewa za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bisa laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma kisan kai da kuma cin zarafin ‘ya mace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *