Budurwa mai shekaru 70 da bata taba saduwa da na miji ba, tana meman mijin aure.

Wata budurwa ‘yar shekara 70 ta ba da labarinta ga Afrimax.

Alphonsine Tawara bata taba samun lokacin saduwa da ɗa na miji ba saboda ta maida rayuwarta wajen kula da kannenta. Duk da shekarunta na girma, septuagenarian tana so ta gyara lokacin da ya wuce mata.

A yayin hirarta, Alphonsin ta ce ita kadai ce ke kula da ‘yan’uwanta. Ta so su gama karatunsu su samu rayuwa mai kyau kafin ta yi aure.

“Har yanzu ban yi aure ba saboda ban sami wanda ya dace da ni ba. Amma sa’ad da nake ƙarama, maza da yawa sun bi ni don neman aurena, amma na ki yin aure kafin ’yan’uwana su kammala karatunsu domin ni ne nake kula da su.

Maza sukan nemi aurena sai in ce musu a’a saboda ina son in fara kula da rainon yan uwana sannan in yi aure daga baya,” inji ta.

Sai dai kash, shekaru sun kama ta, yau da ta shirya yin aure, maza ba sa zuwa wurinta.

Tace “Idan na sami miji zan yi aure. A shirye nake in zama mata kuma in koma wurin mijina,” in ji Alphonsin.

Alphonsin, malamar da ta yi aiki musamman a makarantun mishan na Katolika da yake bata da yaro ta dauki wata dalibarta a matsayin ‘yarta

“Ba ni da yaron da na haifa, amma ni ce uwar ‘ya’ya da yawa. »

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *