SHARHI

Rayuwa kenan kalli yan kannywood da suka rasa rayukan su a shekarar 2022 da kuma cututtukan da silar rasuwar su.

Daga kafa matsana’antar kannywood a shekarar 1990 kawo yanzu ta rasa da yawa daga cikin manyan jarumanta da suka kafa tarihi a matsana’antar, a yau dai mun kawo muku jerin jaruman na kannywood da suka rasa rayukansu a shekarar 2022.

1. NURA MUSTAPHA WAYE

 

Nura ya rasu ne a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya an kuma yi jana’izarsa da misalin karfe 11 na safen 3 ga watan july 2022

Nura Mustapha, darakta ne da aka dade ana damawa shi a masana’antar ta Kannywood.

Fim din Izzar So na daga cikin fina-finai masu dogon zango da suka fi karbuwa a tsakanin masu bibiyar fina-finan masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya.

Kiyasi da aka yi a baya-bayan nan, ya nuna cewa fim din shi ne ya fi yawan masu kallo a dandalin YouTube da ake nuna fim din.

A daren ranar da zai rasu Makusantansa sunce sun rabu da shi lafiya a daren jiya, amma kamin wayewar gari sai aka tadda gawarsa, amma ba’a san silar rasuwar tasa ba har yanzu.

 

2- YAHAYA UMARA MALUMFASHI KAFIN GWAMNA

Allah yayi wa jarumin kannywood na cikin shirin kwana casa’in Alhaji Umaru Malumfashi wanda aka fi sani da “KAFI GWAMNA” rasuwa ne a ranar 27 sep 2022

ya yi fama da jinya na tsawo watanni, inda a mako daya kamin rasuwar tasa ne ya nemi addu’a daga Al’ummar musulmi dangane da halin rashin lafiya da yake ciki.

Jarumi Abba el mustapha yana daya daga cikin mutanen da suka fara bayyana rasuwar tasa a shafinsa na Instagram da facebook inda ya rubuta.

Bayan wannan ya kara da wani rubutu na yaba halayyan kafi gwamna inda yace:

Kafi gwamna kafin rasuwar dai ya kasance tsohon jami’in Hukumar Custom, kuma ya na daya daga cikin dattawan masana’antar kannywood.

Marigayin ya shahara da sunan Kafi gwamna ne saboda rawar da ya taka a shirin Kwana Casa’in mai dogon zango wanda kafar Talabijin ta Arewa 24 ke haskawa.

Kafin rasuwar tasa da ya dan yi rashin lfy aka je da shi asibiti sai ba’a gano abinda take damunsa ba

“Sai kuma daga baya aka sake yin bincike, sai aka gano wani kari ne ya fito a mafitsarar sa,don haka sai aka shirya za a yi masa aiki. Saikuma aka gano shi wannan karin idan yana mataki na 40 ne za a iya cire shi, to shi kuma nasa ya kai har 200 da wani abu, don haka su kace sai an fara yin wani aiki a mataki na farko sannan za a yi na biyun da shi ne za a cire, da aikin farko ne kamin a kai na biyu Allah ya karbi rayuwarsa.

 

3- SA’ADU ADO GANO (BAWO)

Allah yayiwa Jarumin Barkwanci SA’ADU ADO GANO Wanda akafi sani da (ƁAWO) rasuwa a ranar 23 ga watan nuwamba, kuma tuni akayi janaizarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar.

Bawo dai yana daya daga cikin Manyan Jaruman Barkwanci wanda suke gudanar da harkokinsu na wasan barkwanci tare da marigayi rabilu musa ibro

Ya kwashe shekaru da dama yana wannan Harkar wanda kusan suna cikin zubin farko farko da marigayi rabilu musa ibro ya fara dasu, Film dinsu na karshe da marigayin shine fim din karangiya wanda akayishi a babban Birnin tarayya abuja tare da wasu Fitattun Jaruman kudancin Nigeria.

Kamar Dai yadda aka sani a yanzu harkar Finafinan barkwanci taja baya matuka, Kasancewar yawancin jarumanta sun kwanta dama wanda a karshe kuma Jigon nata watau marigayi Rabilu Musa ibro Shima ya cimma sa’a.

4- MAHMUD RAS

An sanar da rasuwar Mahmud Ras. Jarumin ya rasu ne a ranar Asabar 15 ga watan Janairu, 2022, bayan gajeriyar rashin lafiya. Tuni dai a lokacin aka gudanar da jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Har zuwa rasuwarsa, ya kasance fitaccen mamba a kungiyar ‘yan wasan kwaikwayo ta Kannywood da kuma masu daukar hoto a Najeriya wato (MOPPON).

Ya kasance daya daga cikin ’yan wasan barkwanci a Kannywood inda da yawa daga cikin abokanan sana’ar sa sun yaba da halayyar ga yawan murmushi.

Kamin rasuwarsa tasa da dan makonni an ganshi a wani rangadi da taurarin Kannywood suka yi domin karrama wani dan siyasa,

Hakika masana’antar ta yi hasarar tauraro mai hazaka wanda ba zai taba cika gurbinsa ba.

Allah yajikansu Yasa Aljanna ce Makomar muma idan namu tazo Allah yasa mu cika da imani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button