LABARAI

Ƴan sandan Sifaniya sun kama mutum uku kan cin zarafin Vinicius Jr

Ƴan sandan Sifaniya sun kama mutum uku kan cin zarafin Vinicius Jr

Vinicius Jr ya fuskanci kalaman wariyar launin fata a lokuta daban-daban a kakar wasa ta bana.

Ƴan sanda a Sifaniya sun kama wasu mutane uku masu goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Valencia bisa zarginsu da cin zarafin dan kwallon kungiyar Real Madnid Vinicius Junior ta hanyar kalaman wariyar launin fata.

Ƴan sandan Sifaniya sun kama mutum uku kan cin zarafin Vinicius Jr

Photo:Ƴan sandan Sifaniya sun kama mutum uku kan cin zarafin Vinicius Jr

Daga cikin mutanen uku har da wani bakar fata, sanna kuma ƴan sandan sun sanar da kama wasu mutane hudu da ake zargi da rataye mutum-mutumin Vinicius din.

Lamarin ya janyo ka-ce-na-ce a Brazil, sannan gwamnatin kasar ta bukaci ganawa ta musamman da ministocin Sifaniya da masu gabatar da kara da kuma hukumar kwallon kafar kasar.

A lokacin karawar Valencia da Real Madrid ne aka ci zarafin Vinicius, wanda karon farko kenan da aka ba shi jan kati a tarihin sana’arsa ta ƙwallo.

Ɗan wasan mai shekara 23 ya fuskanci kalaman wariya da na cin zarafi karo da dama a La Liga a kakar nan.

An dan dakatar da karawar a zagaye na biyu, bayan da dan kwallon Real din ya nuna bacin ransa kan kalaman wariyar da magoya bayan Valencia suka dinga furtawa a filin wasan.

Daga lokacin ne ransa ya baci har ta kai da aka ba shi jan kati a fafatawar da aka ci Real 1-0, karo na takwas da ta yi rashin nasara a La Liga a bana.

Ita kuwa Valencia, wadda ta ci wasan ta yi sama zuwa ta 13 da tazarar maki biyar tsakaninta da ‘yan ukun karshen teburin La Liga.

Yanzu haka dai ana jiran hukumomin domin ganin irin hukunci da zata yankemusu.

Batareda ɓata lokaciba zamu kawomuku yanda lamarin ya kaya bayan yankemusu hukunci da ya dace dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button