FATI MUHAMMED da LAWAL AHMAD
A wata tattaunawa da gidan labarai na bbc hausa da suka yi da jarumi lawan ahmad a shirin su mai suna daga bakin mai ita.
A wata tambaya da aka masa na cewa ya taba soyayya da wata jarumar kannywood sai ya bayyana cewa yayi soyayya da jaruma fati muhammed na tsawon lokaci wanda har an kai ga maganar aure amma daga karshe allah bai tabbatar da al’amarin ba.
HADIZA GABON da NAZIRU SARKIN WAKA
Shi dai naziru an san shi da yawan kushe yan film mata da maza musamman mata da yake nuna yawancin marasa kunya ne, hakan yasa ba’a taba sammanin zai iya soyayya da tawa jarumar kannywood din ba.
A wani a wani bidiyo da naziru sarkin waka ya cire kwananan kan wata takaddama da suke da shi da wasu jaruman kannywood, a bidiyon ya bayyana cewa ya taba soyayya da jarumar kannywood HADIZA GABON wanda a baya ba kowa ne yasan da hakan ba,
SANI MUSA DANJA da MARYAM JAN KUNNE
Maryam jan kunne ta kasance tsohuwar jarumar kannywood ce da ta koma masanaantar kwanannan bayan mutuwar aurenta. a finafinan da, maryam jan kunne da sani danja ansha kallon su suna yawan fitowa a finafinai tare amma a waccan lokacin mutane da yawa basu san cewa da akwai soyayya a sakanin su ba, sai awata hira da bbc hausa suka yi maryam jan kunne ta bayyana cewa ta taba yin soayya da jarumi sani musa danja.
MUSTAPHA NA BURASKA da HADIZA KABARA
Dan wasan barkwanci mustapha naburaska a wani hira da jaridar BBC hausa tayi da shi ya bayyana cewa yana da mata guda sannan da aka tambaye shi yana da niyar kara aure yace eh yana da niyar kara aure kuma wacce yake sa ran aura ita ce Jaruma HADIZA KABARA.
ADAM A ZANGO nafisa fati washa ummi rahab
a abinda ya bayyana a duniya jarumi adam a zango a shi kadansa yayi soyayya da yan mata uku a kannywood su ne kamar haka nafisa abdullahi fati washa ummi rahab.
Soyayyar nafisa abdullahi da adam a zango soyayya da aka yi ta da kowa sai da yasan da soyayyar su domin nafisa abdullahi kusan a ko ina tana bayyana soyayyar ta ga jarumin adam a zango.
Shi kuwa soyayyarsa da fati washa an tabbatar da shi ne a wani hira da aka yi da shi a shafin bbc hausa inda ya bayyana cewa saura kiris a baya ya auri jaruma nafisa abullahi da fati washa.
Sannan soyayyarsa da ummi rahab ya bayyana ne bayan wani hatsaniya da suka samu a sakanin su wato ummi rahab da adam a zango sai wani da aka bayyana dan uwa ne ga ita jarumar ummi rahab ya fito ya bayyana cewa adam a zango yayi soyayya da ummi rahab harma an shigo da maganar aure a sakanin su a baya amma daga baya shi adam a zango din ya janye a ta nashi bangaren.
SADIYA GYALE DA BABALLE HAYATU
Baballe hayatu da sadiya gyale akwai soyayya a sakaninsu a baya a yadda binciken mu ya gano.
Kishin-kishin din soyayyar ta su dai ya kara karfi ne bayan da wasu hotunan su suka fita a kafafen sadarwar zamani dauke da su cikin irin shiga ta ma’aurata ko kuma ta masu shirin aure.
A shekarar 2016 inda wani dan kannywood ya wallafa cewa baballe da Sadiya gyale sun yi aure inda aka yaɗa labarin a duniya, daga karshe baballe yazo ya karyata batun inda yace raha ce kawai amma basu yi aure ba.
Yanzu da ake ciki dai baballe hayatu bai taba yin aure ba ita kuma sadiya gyale ta fita daga gidan mijinta da ta aura a baya.
BALARABA MUHAMMAD DA SHU’AIBU LAWAN KUMURCI
Su sun kai ga aure amma basu kai ga tarewa ba.
Balaraba Muhammed da shuraibu lawan kumurci a tarihin kannywood ba’a taba samun masoya kamar su ba, suna bayyanawa zunar soyayya a duk inda suka je, hakan yasa a lokacinsu duk duniyar kannywood aka san da soyayyar tasu, an taba yiwa balaraba Muhammad tambaya a wani tattaunawa da aka yi da ita kan cewa ya take soyayya da dan daba nan tayi murmushi cikin fuskar kunya tace a’a wannan halayyar na dabanci a Film kawai yake yinta amma a zahiri ba haka yake ba mutumin kirki ne Abar mata masoyinta.
Sannan gabanin aurenta da shuraibu lawan kumurci yayi, sai da tayi wani waka na ban kwana ga masoyanta da kuma yaɓa shi mijin da zata aura shuraibu lawan kumurci, bayan an daura aurensu ana kan kaina gidan mijinta tayi hatsari a mota Allah ya karbi rayuwar balaraba Muhammad, tabbas a lokacin kumurci ya shiga tashin hankali sosai kan rashin masoyiyarsa da yayi.