Daga shekarar 1998 zuwa shekarar 2021 jaruman kannywood da yawa sun rasa rayuwakan da baza iya cewa ga iya adadin su ba.
A yau dai mun kawo muku bayanai kan jaruman kannywood da suka rasu 2021 da kuma cututtukan da suka yi silar rasuwar su.
1- Sani sk.
Sani sk ya kasance jarumi ne da ya dau shekaru da dama ana damawa da shi a masana’antar kannywood, kafin shigar shi kannywood ya kasance mawaki ne mai yabon mazon Allah SWA.
Sani sk kafin rasuwarsa yayi fama da rashin lafiya na sama da shekaru 3. A baya kafin rasuwarsa sani ya fito ya nemi taimakon jama’a kan rashin lafiya da yake fama da shi, a lokacin an yi ta yaɗa labaran karya wai ya mutu, inda shi da kanshi yafito ya karyata labarin mutuwar tasa, daga lokacin bai wuce watanni biyu ba Allah ya karbi rayuwarsa.
Sani sk ya rasuwa a ranar laraba 15 ga watan Disamba shekarar 2021 ya rasu a sanadiyar ciwon suga da ya haifar masa da ciwon hanta da na koda.
2- Zainab booth
Zainab booth ta kasance tsohuwar jarumar kannywood da suka goya masana’antar tun yana jiriri.
A kwanakin baya ne dai kamin rasuwarta marigayiyar ta yi fama da rashin lafiya lamarin da ya kai har an yi mata aiki a kwakwalwa, kamar yadda ‘yarta Maryam Booth ta dinga wallafa hotunan a shafukan sada zumunta.
Marigayiyar ta kasance daya daga cikin taurarin Kannywood da ‘ya’yanta uku suka kasance su ma taurari…
Ta rasu ne a birnin Kano da daren Alhamis, ran 2 ga watan 7 shekarar 2021, Allah ya karbi rayuwarta tana da shekaru 61 a duniya.
Ta rasu ta bar ‘ya’ya hudu, maza biyu da mata biyu, wato Umar, sai Amude da Maryam da kuma Sadiya, sai jikoki guda biyu.
Ita dai marigayiya zainab booth an bayyana cewa ciwon kyakkyawa da tayi ta fama da shi yayi sanadiyar rasuwar ta .
3- Isyaku forest
mawakin siyasa isyaku forest yana daya daga cikin mawaka da suka yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wakoki a lokacin yakin neman zabe.
Fitacciyar wakar da Forest da ya fito a ciki wacce aka yi wa Buhari da jam’iyyar APC ita ce “Gaskiya Dokin Karfe.” wacce ta samu karbuwa a wajen masoyan jam’iyyar gabanin zaben 2019.
A shekarar 2020, an yanke wa Forest kafa bayan tsawon lokaci da ya kwashe yana fama da rashin lafiya.
A ranar 4 ga watan Satumbar 2021 Forest ya rasu.
Anji labarin cewa shugaban kasa Muhammadu buhari ya Turo da wata tawaga domin yiwa iyalan forest da yan uwa da abokai ta’aziya.
4- Ahmad Tage
JARUMIN barkwanci kuma daɗaɗɗen mai ɗaukar hoton bidiyo (cameraman) a Kannywood, Malam Ahmad Aliyu Tage ya rasu ran 13 ga watan sep 2021
Allah ya karbi ransa ya na da kimanin shekaru 55 a duniya, kuma ya bar ‘ya’ya 21 da matan sa na aure guda biyu.
Ɗimbin mutane, ciki har da abokan sana’ar sa ‘yan fim, sun halarci sallar jana’izar sa wadda aka gudanar a gidan sa da ke unguwar Sheka Ƙarshen Kwalta.
Dan uwan marigayin Ahmad mai suna Umar ya bayyana cewa marigayin ya sanar da shi cewa wannan cutar ba ta tashi ba ce, ya ke cewa in ya mutu a yafe masa.
Tage ya rasu ne a asibiti a Kano bayan yayi jinyar ciwon bugun zuciya da ya samu.
5- Kaka ta bawa
Hajiya Binta tarauni wacce aka fi sani da kaka tabawa a cikin shiri mai dogon zango da tashar arewa 24 take gabatarwa mai suna DADIN KOWA jarumar ta rasu ran 11 ga watan Maris 2021. hajiya Binta dai ta bada gudunmawa ta hanyar fitowa a da tayi a matsayin kakar WiZi a shirin ta dadin Kowa amma har yanzu b
a’a bayyana ciwon da yayi sanadiyar mutuwar ta ba.