SHARHI

Kalli jerin yara da yan kidinafin suka yi masu kisan gilla bayan sun sace su.

Husnah, shekara tara – Zariya

Ana tsaka da tashin hankalin kisan Hanifa ne sai kuma labarin kashe wata yarinya Husnah mai shekara takwas a Zariya da ke jihar Kaduna ya fara yaɗuwa.

BBC ta tuntuɓi mahaifin Husnah, Alhaji Wa’alamu Uban Dawaki, ya kuma tabbatar da cewa an sace ƴarsa ne tun a ƙarshen shekarar da ta gabata, kuma ta shafe kwana 41 a hannun waɗanda suka sace ta.

Sun nemi kuɗin fansa kuma mun aika musu har naira 3,549,000, amma bayan aikawar ba su sako ta ba.

“Daga baya jami’an tsaro suka duƙufa aikinsu suka kuma gano wanda ake zargi da hakan, wanda maƙwabcina ne ga gida ga gida.

“Ya amsa cewa ya sace Husnah ne a ƙofar gida da misalin ƙarfe biyu na rana ta je sayen katin waya,” in ji Alhaji Wa’alamu.

Mahaifin yarinyar ya ci gaba da cewa wanda ake zargin ya tabbatar wa ƴan sanda cewa tuni shi da abokan harƙallarsa sun kashe Husnah har ma sun binne ta a wani waje.

“Amma har yanzu ya ƙi faɗar inda ma suka binneta don mu tono mu ga gawarta mu sake suturta ta. Sannan ya ƙi bayyana mana sauran abokan hulɗar tasa.”

Aisha Sani – Kano

A watan Yunin 2019, an sace wata yarinya mai suna Aisha Sani a Unguwar Tudunwada da ke cikin birnin Kano.

Wata mata ce aka yi zargin ta sace Aisha a hanyarta ta komawa gida bayan tashinsu daga makarantar Islamiyya, kuma mako biyu bayan haka ne aka tsinci gawar Aisha.

Aisha na tafiya gida ne tare da ƴan uwanta yayin da wata mata, wadda ta rufe jikinta ruf har fuska, ta ɗauke ta. Ba a tuntuɓi iyayen Aisha ba har tsawon kwana uku bayan sace ta.

Sun nemi a ba su naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa kuma suka buƙaci mahaifiyar yarinyar ce za ta kai kuɗin.

Daga baya dai da aka tsananta bincike, an tsinci gawar Aisha an daddatsa ta aka jefar da gawar.

Babu tabbas kan me ya faru tun bayan hakan ta fannin binciken makasanta da batun shari’arsu.

Hanifa mai shekara biyar – Kano

Kisan Hanifa ya ɗaga hankalin al’umma

Kisan Hanifa shi ne na baya-bayan nan da ya ɗagawa mutane hankali sosai a shafukan sada zumunta da ma tsakanin waɗanda ba sa amfani da shafukan.

An sace ta tun ranar 4 ga Disamban 2021 a hanyarta ta komawa gida daga islamiyya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu mutane ne suka ɗauke ta a A Daidaita Sahu suka tafi da ita. An yi ta nema da cigiya amma sai bayan kwana 46 aka samu jin ɗuriyarta.

Ko a lokacin ma ba a samu Hanifa a raye ba, don tuni wadanda suka sace tan sun kashe ta ta hanyar ba ta maganin ɓera da yi mata gunduwa-gunduwa tare da saka ta a cikin buhu suka binne ta a makarantar da ta zam can take karatun boko.

Wanda ake zargi da aikata wannan ta’asa ba wani ba da ya wuce malaminta a makarantar bokon, kuma mamallakin makarantar, wanda shi da bakinsa ya shaida wa ƴan sanda batun.

Ya kuma raka su inda ya binne ta har aka tono gawar tata aka sake yi mata sutura.

Tuni ƴan sanda sun miƙa lamari ga kotu, inda za a fara sauraron ƙarar ranar 2 ga Fabrairun 2022.

Za a iya cewa labarin Hanifa ya karaɗe ciki da ma wajen Najeriya, kuma mutane sun zuba ido don ganin irin hukuncin da hukumomi za su yanke wa mutumin da sauran abokansa biyu da suka taya shi wannan aika-aika.

Al’ameen adamu fataskum

A shakarar 2019 wani yaro mai shekaru 4 ya bata a garin Potiskum dake jihar Yobe, daga baya kuma sai abin ya zama ashe ba bata yaron ya yi ba, masu garkuwa da mutane ne suka dauke shi, inda suka buka ci kudin fansa har Naira Miliyan 8 sannan su sake shi. A karshe dai an kama wadanda suka yi garkuwa da yaron, amma kuma sun kashe yaron, bayan sun cire wasu sassa na jikinsa.

mahaifin al’ameen mala adamu ya bada labarin batan yaron nasa yace: To Yaro na mai suna Al-amin, mai shekaru 4 da wata 3, ya bata ne ranar 17 ga wannan wata na Afrilu. Da magariba ne yaron ya fita, ya zauna a kofar gida. To da muka ga shiru bai dawo ba, sai muka fara nemansa a gidajen maqwabta da gidajen masu unguwanni, har zuwa wayewar gari dai ba a samu yaro ba. Haka dai muka ci gaba da nemansa har zuwa gidajen ‘yan’uwanmu. Daga qarshe dai sai muka je muka sanar a hukumar watsa labarai ta qaramar hukumar Potiskum da gidan Rediyo aka yi ta cigiyar yaro, amma ba a same shi ba. To da daddare ina zaune a gida, sai ga wani yaro ya shigo da takarda, a jiki an rubuta Maman Haidar (Matata kenan) da kuma lambar waya a rubuce a jikin takardar. (Kwana daya da batan yaron kenan).
Da yaron ya shigo, sai ya ce ina Maman Haidar? sai nace masa ga ta nan. Sai ya ce wai gashi ta kira wannan lambar. Sai na cewa yaron waye ya turo ka da wannan takardar? Sai ya ce min yana waje. Sai nace masa to muje wajensa. Muna fita, sai muka ga babu kowa, wanda ya turo shi da takardar ya gudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button