KANNYWOOD

Kalli motocin kece raini da naziru sarkin waka yake

Naziru sarkin waka mawaki wanda ya shahara sosao a duniyar hausawa, yana daya daga cikin mawakan hausa sa suka fi kudi a duk fadin Nigeria, inda wasu na cewa yana cikin mawaka uku da suka kudi a mawakan hausa.

Hakan yasa yana siyan manyan motocin alfarma domin kece raini.

Wannan itace motar da jarumin yake hawa kafin 2020, wannan motar mai suna AMG G-WAGOON BENZ ta kai a kalla dalar amurka $120,000 wanda yake daidai da naira ₦138,800,000.

Sai kuma a 2020 mawakin ya sake wasu sabbin motoci na azo a gani kirar Lexus guda biyu wanda aka kera a shekarar ta 2020.

Kamin ya siyo motocin sai da ya saka hotunan motocin a shafinsa na Instagram yana neman shawarar wanne daga ciki zai siyo, nan mafi yawa daga cikin mutanen da suka bashi amsa cewa suka yi ya siyo duka biyu motocin domin yafi karfi su, kuma haka aka yi sai da ya siyo su.

Bayan neman shawara dasu kwanaki sai ga mawakin ya ɓare dukka biyo motocin kirar Lexus Ls da Lx, inda kudin motar biyu ya kai dalar amurka, $180,000 wanda daidai yake da ₦205,200,000.

Wannan daya daga cikin motocin nasa ne a kofar sabon gidan sa da ya gina.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button