LABARAI

A inda ya kamata kayi amfani da kalaman soyayya ta yadda mace zata haukace a kanka

Kalaman soyayya

A Ina Ake Amfani Da Kalaman Soyayya ?

Yawancin mutane musamman samari sukan yi min tambayoyi kamar haka:

  1. Wadanne kalaman soyayya zan ringa fadawa mace ta so ni?
  2. Kana da kalaman soyayya masu zafi?
  3. Wadanne kalamai ne mata suka fi so?

Amsa anan shine babu wani kalami mai zafi da zaka fadawa mace ta soka saboda shi, hasali ma ai ba ko yaushe ake fadawa mace kalaman ba. Dadin dadawa kuma kalaman soyayya basu da amfani a sabuwar soyayya wacce bata dade ba, sunfi amfani a soyayyar da ta riga tayi nisa. Misali anan shine ace saurayi ya ga budurwa yana so sai yaje ya fara gaya mata:

“Assalamu alaiki ya tauraruwar taurari, tun daga nesa na hango hasken walqiya da walwalin annurin fuskarki mai kama da farin wata daren goma sha uku, a gaskiya na kamu da dinbim gigitacciyar soyayyarki tunda na hango ki, zuciyata ta riga ta sallama miki jiki da ruhina, duk duniyar nan. . .”

Haba Malam?! In dai mace mai hankali da tunani ce daka ganinta har ka shiga cikin kogin soyayyarta kayi nisa haka bayan baka san wacece ita ba, baka san yaya halinta yake ba, baka san ko mutuniyar kirki ce ko a’a ba, tasan ba ita tafi kowa kyau a duniya ba. . .tasan cewa KARYA KAKE! DADIN BAKI KAKE MATA dan ta so ka!!!

Daga farkon soyayya zuwa kafin tayi nisa babu wani kalami mafi tasiri da zaka dinga gayawa mace ka sace zuciyarta wanda ya wuce ka dinga fada mata gaskiya! Komai zaka fada mata sai ka gaya mata gaskiya, karka sake kayi mata qarya!

Abu na biyu kuma shine sai ka dinga fada mata irin yadda kake sonta (misali: ina sonki har cikin zuciyata); kada ka wuce gona da iri (misali: ina sonki tun daga cikin jijiyoyin jinin jiki da dukkan. . .) ba yanzu ake buqatar wadannan ba!

Sai kuma ka dinga gaya mata yadda kake tunawa da ita idan bakwa tare, ko idan kaje kwanciya dss, amma kada ka dinga cewa wai ka kasa cin abinci saboda tunaninta (ashe zaka mutu da yunwa kuwa!), haka zaka yi ta rainon soyayyar tata har sai tayi qarfi.

Kalaman Soyayya

A lokacin da soyayya ta riga tayi qarfi; bayan kun amince da halayen juna kun yarda da kuyi soyayyar, to daga nanne zaka iya fara amfani da kalaman soyayya duk yadda kaga dama, ko ma abinda ka fada ba zai yiwu a gaske ba dai tasan cewa kana sonta da gaskiya, ta hakanne ma zai sa ta qara sanin irin girman son da kake yi mata ita ma sai ta qara sonka.

A takaice dai ana amfani da kalaman soyayya ne a soyayyar da ta riga tayi nisa bayan an gina ta akan gaskiya. Aikawa da saqwannin kalaman soyayya ta wayar salula (text message) yana da matuqar muhimmanci a soyayya kasancewar masoyin ko masoyiyar zata dinga dubawa a duk lokacin da taji nishadi, ba kamar na magana ba wanda da an fada ya wuce!

Hmm, kun san me na aikawa da maso nayi:

“Sarauniyar birnin zuciyata a duk lokacin da na rufe idona sai in hango ki sanye da wasu fararen kaya masu adon alharini cikin wani lambu ma’abocin korayen ganyayyaki masu dauke da furanni kala-kala, a gefe ga wani …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button