Tattaunawa da Lawan Ahmad akan rayuwarsa mai mahimmanci da baku sani ba.

TAKAITACCEN TARIHIN KA?

Sunana lawan ahmad jarumi a masana’antar finafinan hausa na kannywood wanda aka fi sani da umar hashim a wannan lokacin a cikin film din izzar so, kuma ni mutumin katsina ne a cikin garin bakori local goverment a jihar katsina a unguwar Tofa aka haife ni, a garin nayi primary school dina da kuma secondary school zuwa jss3 bayan nan na samu transfert zuwa kano na shiga ss1,

Daga nan na fara harkar film kadan-kadan, sai kuma na tafi FCI na Kano nayi diploma in public admin, bayan nan saina tafi university na maitama sule, daga nan naci gaba da harkar film dina,

KANA DA SHEKARU NAWA DA HAIFUWA ?

Ina da shekaru talatin da takwas (38)

YA AKA YI KA SHIGA HARKAR FILM?

Abinda yasa na shiga harkar film, film yana birgeni sannan ina kallon ta tin ina yaro a kauye, a lokacin idan muna wasa sai ni in ringa kwaikwayon DanGugaji ina irin acting dinsa, har mutane sun fara kirana da Dandugaji a lokacin, sai kuma nazo kano naci gama da karatu na, sai kuma harkar film din yaci gaba da bani sha’awa, idan yan film suna acting ina zuwa kallon su, daga na sai na fara jin ina son shiga harkar sosai, sai watarana Allah ya hada ni da marigayi Ahmads Nuhu, shine ya dauke ni ya kaini FKD production,

Kaji ta inda na fara harkar film kuma na fara film ne a karshen shekarar 1999, sannan na fara fitowa ne a wani film mai suna Izina sau daya aka nuna ni a film din, daga nan kuma sai muka zo muka yi wani film da Ahmad S. Nuhu mai suna SIRADI na fito a matsayin Bello a wannan film, nan mutane suka fara sani na, duk inda naje mutane suna kirana Bello, ni kanin Ahmed ne a film din, anan na fara harkar film har Allah ya kawo mu wannan matsayin.

WANE FILM NE KAFI SO A FINAFINAN KA?

Duk film din da nayi ina son shi amma yanzu na fi son Izzar so series wanda nake yi a yanzu, kuma shine yanzu ake kallo a shafin Youtube.

ME YASA KAFI SON IZZAR SO?

Saboda wani al’amari ne ya faru wanda ni ina kiransa da ikon Allah, saboda ada finafinan mu na baya k7 ake yi aka dawo yin CD aka dawo yin DVD, wanda duk wani ci gaba mu kannywood a baya-baya muke samun sa, to kamar yanzu wannan abinda yasa nace nafi son shi wato haja ce da take hannunka wato kafa ta youtube, wanda a baya bamu san shi ba munyi watsi da shi, amma cikin ikon Allah sai nace bari nayi sacrify mu fara mu gani, cikin ikon Allah da muka yi kuma sai ya samu karbuwa a wajen jama’a, yanzu ba sai nayi film na kai kasuwa ba, ba sai nayi film na kira wani dan kasuwa ba nace yazo ya siya ba, ko ina yi film ina tallatawa nayi film, yanzu idan nayi film dina a Youtube nake daura shi, kuma ta wannan hanyar zan samu abinda zai ishe ni har da riba,

YA AKA YI KA SHIRYA KUMA KAI NE JARUMI A FILM DIN?

Yawancin finafinai indai irin namu ne, ba na turai ba, saboda tsarin su da namu sun sha bamban, kuma su ci gaba da suka samu a harkar finafinai mu bamu samu ba, mu anan wajen mu zaka iya hada duka biyu, kuma ni actor ne an sanni, kuma film din nan series ne saboda kar a samu matsala nace bari ni na jagoranci film din, daga baya duk wanda zai taho ya kasance a baya na, kaga hakan zai yi wahala a samu matsala.

ZA’A IYA GAMA SERIES DIN IZZAR SO KUWA?

Ni bana ganin cewa za’a iya gama shi, indai har baza’a gaji da kallo ba, mu kuma baza mu gaji da yi ba, saboda ina yi wa series din Izzar so kallon makaranta.

DA WANI ACTOR KO ACTRESS KAFI SON A HADA KU A FILM ?

Alhamdulillah ni ina kishin masana’antar ta kannywood, dalili shine duk wanda aka hada ni aiki da shi indai na film ne, zan tsaya nayi tsakani na da ALLAH ko da wanene, mutumin ko yanzu yazo kannywood ko ya dade a kannywood saboda duk wani film din da aka ce inyi indai ban yarda da shi ba to bazan yi ba, amma indai na yarda da shi to zan yi shi.

KA TABA YIN SOYAYYA DA WATA ACTRESS A KANNYWOOD?

Eh, na taba yin soyayya da Fati Muhammed har maganar aure tadan shiga tsakanin mu, amma da yake Allah bai kaddara ba sai muka watse, ita kadai kawai na taba soyayya da ita a kannywood.

ME YAKE SA KA FARIN CIKI?

Abinda yake sa ni farin ciki shine, yadda a wannan lokacin mutane suke min addu’a kan wannan series din da nake na izzar so.

ME YAKE SA KA BAKIN CIKI ?

Abinda yake sa ni bakin ciki shine, idan muka zo wajen aiki sai naga mutane basa maida hankali wajen aikin nasu, kamar shine yafi sa ni bakin ciki.

ANCE KANA TAKARA DA SIYASA

Kafin na fara series din izzar so na fara taba yin takara a 2019 na dan majalisar tarayya mai wakiltar Bakori, daga baya na bar maganar takarar.

YA BATUN IYALI ?

Ina da mata kuma shekara 14 da aure ina da yara hudu, maza biyu mata biyu.

MUN GODE DA TATTAUNAWA DA KAYI DA MU.

Nima na gode.

TAKAITACCEN TARIHIN KA?

Sunana lawan ahmad jarumi a masana’antar finafinan hausa na kannywood wanda aka fi sani da umar hashim a wannan lokacin a cikin film din izzar so, kuma ni mutumin katsina ne a cikin garin bakori local goverment a jihar katsina a unguwar Tofa aka haife ni, a garin nayi primary school dina da kuma secondary school zuwa jss3 bayan nan na samu transfert zuwa kano na shiga ss1, daga nan na fara harkar film kadan-kadan, sai kuma na tafi FCI na Kano nayi diploma in public admin, bayan nan saina tafi university na maitama sule, daga nan naci gaba da harkar film dina,

KANA DA SHEKARU NAWA DA HAIFUWA ?

Ina da shekaru talatin da takwas (38)

YA AKA YI KA SHIGA HARKAR FILM?

Abinda yasa na shiga harkar film, film yana birgeni sannan ina kallon ta tin ina yaro a kauye, a lokacin idan muna wasa sai ni in ringa kwaikwayon DanGugaji ina irin acting dinsa, har mutane sun fara kirana da Dandugaji a lokacin, sai kuma nazo kano naci gama da karatu na, sai kuma harkar film din yaci gaba da bani sha’awa, idan yan film suna acting ina zuwa kallon su, daga na sai na fara jin ina son shiga harkar sosai, sai watarana Allah ya hada ni da marigayi Ahmads Nuhu, shine ya dauke ni ya kaini FKD production, kaji ta inda na fara harkar film kuma na fara film ne a karshen shekarar 1999, sannan na fara fitowa ne a wani film mai suna Izina sau daya aka nuna ni a film din, daga nan kuma sai muka zo muka yi wani film da Ahmad S. Nuhu mai suna SIRADI na fito a matsayin Bello a wannan film, nan mutane suka fara sani na, duk inda naje mutane suna kirana Bello, ni kanin Ahmed ne a film din, anan na fara harkar film har Allah ya kawo mu wannan matsayin.

WANE FILM NE KAFI SO A FINAFINAN KA?

Duk film din da nayi ina son shi amma yanzu na fi son Izzar so series wanda nake yi a yanzu, kuma shine yanzu ake kallo a shafin Youtube.

ME YASA KAFI SON IZZAR SO?

Saboda wani al’amari ne ya faru wanda ni ina kiransa da ikon Allah, saboda ada finafinan mu na baya k7 ake yi aka dawo yin CD aka dawo yin DVD, wanda duk wani ci gaba mu kannywood a baya-baya muke samun sa, to kamar yanzu wannan abinda yasa nace nafi son shi wato haja ce da take hannunka wato kafa ta youtube, wanda a baya bamu san shi ba munyi watsi da shi, amma cikin ikon Allah sai nace bari nayi sacrify mu fara mu gani, cikin ikon Allah da muka yi kuma sai ya samu karbuwa a wajen jama’a, yanzu ba sai nayi film na kai kasuwa ba, ba sai nayi film na kira wani dan kasuwa ba nace yazo ya siya ba, ko ina yi film ina tallatawa nayi film, yanzu idan nayi film dina a Youtube nake daura shi, kuma ta wannan hanyar zan samu abinda zai ishe ni har da riba,

YA AKA YI KA SHIRYA KUMA KAI NE JARUMI A FILM DIN?

Yawancin finafinai indai irin namu ne, ba na turai ba, saboda tsarin su da namu sun sha bamban, kuma su ci gaba da suka samu a harkar finafinai mu bamu samu ba, mu anan wajen mu zaka iya hada duka biyu, kuma ni actor ne an sanni, kuma film din nan series ne saboda kar a samu matsala nace bari ni na jagoranci film din, daga baya duk wanda zai taho ya kasance a baya na, kaga hakan zai yi wahala a samu matsala.

ZA’A IYA GAMA SERIES DIN IZZAR SO KUWA?

Ni bana ganin cewa za’a iya gama shi, indai har baza’a gaji da kallo ba, mu kuma baza mu gaji da yi ba, saboda ina yi wa series din Izzar so kallon makaranta.

DA WANI ACTOR KO ACTRESS KAFI SON A HADA KU A FILM ?

Alhamdulillah ni ina kishin masana’antar ta kannywood, dalili shine duk wanda aka hada ni aiki da shi indai na film ne, zan tsaya nayi tsakani na da ALLAH ko da wanene, mutumin ko yanzu yazo kannywood ko ya dade a kannywood saboda duk wani film din da aka ce inyi indai ban yarda da shi ba to bazan yi ba, amma indai na yarda da shi to zan yi shi.

KA TABA YIN SOYAYYA DA WATA ACTRESS A KANNYWOOD?

Eh, na taba yin soyayya da Fati Muhammed har maganar aure tadan shiga tsakanin mu, amma da yake Allah bai kaddara ba sai muka watse, ita kadai kawai na taba soyayya da ita a kannywood.

ME YAKE SA KA FARIN CIKI?

Abinda yake sa ni farin ciki shine, yadda a wannan lokacin mutane suke min addu’a kan wannan series din da nake na izzar so.

ME YAKE SA KA BAKIN CIKI ?

Abinda yake sa ni bakin ciki shine, idan muka zo wajen aiki sai naga mutane basa maida hankali wajen aikin nasu, kamar shine yafi sa ni bakin ciki.

ANCE KANA TAKARA DA SIYASA?

Kafin na fara series din izzar so na fara taba yin takara a 2019 na dan majalisar tarayya mai wakiltar Bakori, daga baya na bar maganar takarar.

YA BATUN IYALI ?

Ina da mata kuma shekara 14 da aure ina da yara hudu, maza biyu mata biyu.

MUN GODE DA TATTAUNAWA DA KAYI DA MU.

Nima na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *