Adam a zango dai yayi soyayya da mata masu yawa a kannywood amma ga kadan daga cikin su wayan da yayi soyayya da su kuma da yadda soyayyar tasu ta kasance.
FATI WASHA
Daga shekarar 2018 zuwa 2020 Adam a zango da Fati Washa sun sha soyayya sosai wanda kiris ya rage suyi aure, amma abin bai tabbata ba.
A lokacin da suka yi soyayyar ba kowa bane ya san da hakan ba, sai makusantan su.
Sai a shekarar 2020, adam a zango ya bayyana cewa zai kara aure kuma ‘yar Fim ce zai aura.
inda zangon ya saka hotonsa dana Fati Washa a Profile Picture dinsa na Instagram da alamar zanen Zuciya, dake alamta Soyayya.
Nan masoyansu suka gano cewa ashe akwai soyayya sakanin adam a zango da fati washa kuma akwai alamun cewa ita zai aura.
Tabbas wa’yannan masoyan biyu sun sha soyayya sosai amma Allah bai tabbata auren su ba.
Sannan a wata hira da BBC Hausa suka yi da adam a zango ya bayyana cewa saura kiris ya auri fati washa.
NAFISA ABDULLAHI
A shekarar 2015 Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisah Abdullahi, ta yi ta-maza, inda ta ce tana matukar kaunar abokin aikinta, jarumi Adam Zango.
Tauraruwar — wacce ta bayyana matsayinta a shafinta na Instagram — ta kara da cewa tana fatan Allah zai zaba masu mafi alheri tsakanin ta da shi.
Nafisa Abdullahi da adam a zango dai tun kafin jarumar ta bayyanawa duniya tana son Adam a Zango mutane sun san da cewa akwai soyayya mai karfi a sakaninsu.
Bayan nafisa Abdullahi ta bayyana soyayyar ta ga Adam A. Zango, shi ma ya bata amsa ya ce ya yi matukar farin ciki da abokiyar aikinsa, Nafisa Abdullahi ta ce tana matukar kaunarsa. Sannan shi ma yana kaunar Nafisa yana fatan Allah ya zaba musu mafi alheri a tsakanin su. Nan labarin soyayyar su ya karade duniya. Inda ake sa ran watarana zasu yi aure.
Sai a shekarar 2019 da BBC Hausa tayi hira da nafisa Abdullahi ta bayyana cewa basa tare a yanzu tace Kusan shekaru hudu ke nan ko biyar basa tare, kamar yadda Allah ya hada haka kuma yanzu ya raba su. Zama ne kawai ya zo karshe”.
UMMI RAHAB
Adam A. Zango dai ya nuna wa Ummi Rahab ƙauna tun ta na ƙarama. Ya shirya fim ɗin ‘Ummi’ da ita da nufin mayar da ita fitacciyar jaruma yarinya. An yi wata waƙa a cikin fim ɗin mai taken ‘Kin Zamo Takwara Ummi’, inda Jamila Nagudu ta fito a matsayin mahaifiyar Rahab da Haidar, babban ɗan Zango.
Bayan wasu abubuwan suka faru sakanin UMMI rahab da adam a Zango da yayi sanadiyar rabuwar su, nan wani mai suna Yaseer da yake kamar dan uwa ga Ummi rahab, ya fito ya bayyana cewa a zango yana soyayya da Ummi, inda har manya sun shiga maganar domin ayi auren. Amma daga karshe Adam a zango ya janye a nashi bangaren amma ba’a bayyana dalilin haka da yayi ba, sannan game da wannan maganar da naseer yayi, adam a zango bai fito ya karyata ba, hakan na nuna cewa gaskiya maganar nashi.
Yanzu dai UMMI rahab da adam a zango basa tare, kuma taje aure idan ta auri mawaki Lilin baba
Sannan a karshe adam a Zango ya taba auren jarumar kannywood mai suna Maryam ab Yola daga karshe sun rabu har ta koma harkar Film da take yi kamin yin aurentata da adam a zango.