Tirƙashi:Mawaki Rarara ya fara biyan ƴan sandansa da aka kora albashi
Fitaccen mawaƙin siyasar nan na Nijeriya, Dauda Kahutu Rarara, ya ce ya soma biyan ƴan sandan nan uku da aka kora daga aiki albashinsu.
A wani bidiyo da mawaƙin ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa a ranar 30 ga wata ya tura wa kowa albashinsa.
“Su ma’aikatana da aka kora, na ɗauki nauyin zan ci gaba da biyansu albashi iya yadda ake biyansu, kuma Alhamdulillahi yau ne 30 ga wata, na tura wa kowa albashin shi,” in ji mawaƙin.
Mawaƙin ya kara da cewa har ya mutu zai ci gaba da biyansu albashin da aka saba biyansu.
A watan da ya gabata ne rundunar ƴan sandan Nijeriya ta kori wasu ƴan sanda uku waɗanda suke bai wa Rarara kariya bisa samunsu da laifin saba ƙa’idar aiki.
Jami’an uku da aka sallama sun haɗa da Insifekta Dahiru Shuaibu da Sajan Abdullahi Badamasi da kuma Isah Danladi, TRT Afrika ce ta rawaito mana
Me ya sa aka sallami ƴan sandan?
A kwanakin baya ne wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna ƴan sandan uku suna harba bindiga a sama a garin Kahutu yayin da suke yi wa mawaƙin rakiya.
A nasa bangaren, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa ƴan sandan sun yi harbi ne bayan da suka samu labarin cewa wasu bata-gari za su tayar da tarzoma yana mai cewa ba don nishaɗi suka yi harbi a iska ba.
“Mun je muna rabon abinci a Kahutu, sai wasu bata-gari suka shigo suna neman su tayar da tarzoma, a nan wurin ne muka samu matsala ƴan sandanmu suka yi harbi sama,” a cewar Rarara.
Sai dai daga baya rundunar ƴan sandan kasar ta sallami jami’an uku sakamakon samunsu da laifukan da suka haɗa da amfani da bindiga ba bisa ƙa’ida ba da wuce gona da iri da rashin ɗa’a da kuma ɓata harsashin gaske.
“Wannan lamari ba mugun laifi da rashin kwarewa kawai yake nunawa ba, har da jawo wa rundunar da ma kasa baki ɗaya abin kunya,” in ji rundunar ƴan sandan a sanarwar da ta fitar bayan sallamar jami’an nata.
kucigaba da bibiyar wannan shafin mai albarka domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu.
Abi doka a zauna lafiya