Tabarmar Kunya Da Hauka Aka Naɗeta Idan Kaina Yazakayi ?

Tabarmar Kunya Da Hauka Aka Naɗeta Idan Kaina Yazakayi ?

Tabarmar Kunya Da Hauka Aka Naɗeta Idan Kaina Yazakayi ?

Na dawo gida daga aiki a gajiye liƙis. Na jefar da jakar da ke rataye a kafaɗata, na faɗa kan ɗaya daga cikin kujerun dake falo, domin na sauke gajiyar da na kwaso.

Maman Amir ta yi mini barka da dawowa, sannan ta kawo mini ruwa mai sanyi a kofi. Na fara shan ruwan ke nan sai ga Amir ya shigo falon da gudu yana faɗin, “Baba barka da zuwa.” Ya miƙo mini takardar da ke hannunsa.

Na ajiye kofin ruwa na duba takardar, sai na ga ashe sakamakon jarabawa ne, sakamakon da ya ɓata mini rai matuƙa. Daga cikin darussa tara da ke ƙunshe cikin takardar, darussa uku kacal aka ci hamsin cikin ɗari, saura duka ƙasa da maki hamsin aka samu.

Na dubi matata cikin fushi da ɓacin rai na ce, “Yaushe Amir ya lalace ne haka da zai kawo mini wannan mummunan sakamako. Sakamakon da ba wani daga cikin danginmu da ya taɓa samun irinsa!”

Matata ta fara magana tana cewa, “Saurara ka ji Baban Amir…”

Na katse ta, “Me zan ji, kin riga kin lalata yaro da kallace-kallacen banza da wofi. Abin kunya ne gare ni a ce ɗana ya kawo mini wannan mummunan sakamako.”

Amir da ke tsaye gefe gudu ya tsoma baki ya ce, “Baba a cikin tsohon kabod ɗinka fa na tsinci takardar, lokacin da nake share shi ɗazu, shi ne na kawo maka ita yanzu.”

Na sake duba takardar da ke hannuna da kyau, sai na ga ashe sakamakon jarabawata ce, shekaru ashirin da suka wuce. Na yi kasaƙe ina tunanin abin da zan yi, duk kunya kuma ta rufe ni. Da ma an ce baki shi ke yanke wuya. Saurin fushi kuma shi ke kawo da-na-sani.

Na dubi matata da ɗana ina murmushin yaƙe, na ce musu, “A zamanin da muka yi karatu, samun irin wannan sakamakon sai wane da wane, domin a wancan lokaci harakar ilimi ba ta taɓarɓare ba kamar yanzu. Ba ƙaramin yabo na samu ga wannan sakamako da kuke gani ba.”

Na tashi na shige ɗakina, ina zazzare idanu, wai kada su kawo man raini. Na bar su tsaye sororo suna kallo na. Yo, tabarmar kunya ai da hauka ake naɗe ta.

Tabarmar Kunya Da Hauka Aka Naɗeta Idan Kaina Yazakayi ?

Tabarmar Kunya Da Hauka Aka Naɗeta Idan Kaina Yazakayi ?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *